Tsagerun Taliban sun kai farmaki filin jirgin sama na Afghanistan | Labarai | DW | 08.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsagerun Taliban sun kai farmaki filin jirgin sama na Afghanistan

Rahotanni sun nuna cewa 'yan Taliban sun kai hari kan filin jirgin sama na Kandahar na Afghanistan inda aka yi musamman wuta da jami'an tsaro.

Tsagerun kungiyar Taliban sun kai farmaki a filin jirgin saman garin Kandahar da ke kasar Afghanistan, abin da ya janyo musanyen wuta da fashe-fashe. Mai magana da yawun gwamnan lardin ya ce tsagerun sun samu kutsa kai kofar farko na filin jirgin saman. Babu cikekken bayani kan halin da ake ciki yanzu haka. Sai dai wannan na zuwa kwanaki bayan rade-radin cewa an hallaka shugaban kungiyar ta Taliban Mullah Akhtar Mansour yayin rikici na cikin gida.

Lamarin ya faru yayin da aka fara zaman kasashen yankin a Pakistan domin farfado da shirin zaman lafiya na Aghanistan, domin dakile tashe-tashen hankula da ake samu.