Trump ya yi wa China gugar zana | Labarai | DW | 30.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump ya yi wa China gugar zana

Rikicin cinikayya tsakanin kasashen Amirka da China na ci gaba da janyo matsalolin tattalin arziki tsakanin manyan kasashen biyu na duniya da ke da karfin masana'antu.

Shugaban Amirka Donald Trump, ya sake nanata ikirarin da ya yi cewar China ta fi ji a jikinta a rikicin kasuwancin nan da ke tsakanin kasashen biyu.

Cikin wannan watan na Mayu ne dai shugaban na Amirka ya zargi mahukuntan birnin Beijing da warware alkawuran da suka yi a baya.

Lamarin ya sanya Mr. Trump tsawwala harajin dala biliyan biyu kan kan kayayyakin China da za su rika shiga Amirkar.

Shugaba Turmp ya ce a bayyana take cewar tsananta haraji kan kayayyakin da kasashen biyu suka dora wa juna, ya fara bayyana illoli kan kasar ta China.

Sai dai matakin ya sanya manoman Amirka cikin wani hali na tsaka mai wuya.