Trump ya sanar da Rasha muhimman bayanai. | Labarai | DW | 16.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump ya sanar da Rasha muhimman bayanai.

Shugaban Amirka Donald Trump ya sanar da wasu muhimman bayanan sirri ga kasar Rasha sai dai fadar White House ta musanta da cewa ba gaskiya bane.

Wani babban jami'i a fadar White House ya musanta cewa shugaba Donald Trump na Amirka ya baiyana wasu muhimman bayanai kebabbu dake bukatar sirri ga ministan harkokin wajen Rasha Segei Lavrov a lokacin wata ganawa da suka yi a makon da ya wuce.

Mai baiwa shugaba Trump shawara kan al'amuran tsaro HR McMaster yace shugaban da Ministan harkokin wajen sun yi nazarin wasu bayanai ne da suka shafi barazanar tsaro da kasashen biyu ke fuskanta. O-Ton......

Yace baiyanan da ake yadawa ba gaskiya bane shugaban kasa da ministan harkokin waje sun yi bitar wasu jerin barazana da kasashensu ke fuskanta wadanda suka hada da barazana ta tsaron sufurin jiragen sama. Ko kadan babu wani lokaci da suka tattauna bayanan sirri kuma shugaban kasa bai baiyana wasu ayyukan soji sabanin wadanda aka sani ba.