1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya kai ziyarar ba zata kasar Iraqi

Abdullahi Tanko Bala
December 27, 2018

Shugaban Amirka Donald Trump ya kai ziyarar ba zata ta Kirsimeti ga sojojin Amirka a Iraqi, ziyararsa da ke zama ta farko cikin shekaru biyu na mulkinsa da ya kai yankin da ake fama da yaki.

https://p.dw.com/p/3AfeX
Trump besucht US-Truppen im Irak
Hoto: AFP/Getty Images/S. Loeb

Ziyarar dai na zuwa ne 'yan kwanaki bayan da ya sanar da janye sojojin Amirka daga Siriya mai makwabtaka da Iraqin.

Trump ya yi amfani da ziyarar wajen kare matsayinsa na janye sojojin Amirka daga Siriya matakin da ke shan suka daga bangarori da dama, yana cewa zaman sojojin a Siriya ba zama ne na dundundun ba. A saboda haka sojojin za su dawo gida.


'Yan majalisar dokoki na jam'iyyar Demokrat da Republican sun soki lamirin manufofinsa kan Siriya da cewa da sauran rina a kaba a yaki da 'yan IS.

A hanyarsa ta komawa gida Trump ya yada zango a sansanin sojin sama na Ramstein a Jamus inda ya gana tare da yin musabiha da wasu sojojin Amirka kafin ya wuce zuwa Washington.