Trump na son ya takali Turai kan mayakan IS | Labarai | DW | 17.02.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump na son ya takali Turai kan mayakan IS

Trump ya ce Birtaniya da Faransa da Jamus da sauran kawayensu su zauna cikin shiri na karbar 'yan IS 800 da za su yi wa shari'a don in ta kai makura zai sako su.

Mayakan sojan da ke samun tallafi na Amirka a yaki da IS a Siriya sun bayyana cewa sun tattatare mayakan na IS a wani karamin yanki mara fadi a kusa da koguna da kwazazzabai na Euphrates kamar yadda kwamandan wadannan sojoji ya bayyana a ranar Asabar. Matakin da a fadar Shugaba Donald Trump an taki kawar da su baki daya.

Jiya Furat kwamandan sojojin fafutukar kafa dimukuradiyya a Siriya (SDF) ya bayyana a kauyen Baghouz da ke iyaka da Iraki cewa, mayakan na IS na shan wuta ta ko'ina inda aka yi masu kawanya. Ya ce nan da sa'oi 24 za a samu labari mai dadi.

Shi kuwa Trump da salon yada bayanansa a Twitter ya ce mayakan na IS za su fadi kasa don haka kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus da sauran kawayensu su zauna cikin shiri na karbar 'yan IS 800 da za su yi wa shari'a, don in ta kai makura zai sako su.