Trump ba zai yada corona ba inji Likita | Labarai | DW | 11.10.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump ba zai yada corona ba inji Likita

Likitan fadar shugaban kasar Amirka ya ce Shugaba Donald Trump ba ya cikin hatsarin yada cutar corona, sai dai likitan bai tabbatar ko Trump ya warke daga cutar kwatakwata ba.

Wasu likitocin Amirka sun fara nuna shakku kan matakin binciken likitan Shugaba Trump, tare da zargin neman ba wa shugaban damar fita daga killace kanshi kwanaki goma bayan tabbatar da yana dauke da cutar corona.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da Shugaba Donald Trump ke shirin komawa fagen daga na yakin neman zabe, inda tuni ya gabatar da jawabin farko tun bayan da ya kamu da cutar kusan makonni biyu baya.