Tawagar gwamnoni ta biyu za ta gana da Buhari | Labarai | DW | 25.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tawagar gwamnoni ta biyu za ta gana da Buhari

A karo na biyu cikin mako guda, wasu gwamnonin Najeriya ciki har da na adawa za su gana wa shugaba Muhammadu Buhari wanda ya shafe sama da wata biyu a yana fama da jinya a birnin London na kasar Birtaniya.

Fadar shugaban kasa a Najeriya, ta ce tawaga ta biyu za ta kama hanyar zuwa birnin London na kasar Birtaniya domin ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, abin da wasu ke ganin alamu ne na samun lafiyar shugaban.

Tawagar wadda ke ta gwamnoni bakwai karkashin jagorancin Abdul'azeez Yari, gwamnan jihar Zamfara kuma shugaban kungiyar gwamnonin kasar, ta kunshi gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki biyar da kuma PDP da ke jagorantar adawa su kuma biyu.

Wannan ne dai karo na farko da wani mai adawa da gwamnatin ta Buhari ke shirin tozali da shugaban da rashin lafiyar tasa ya jawo rabuwa da surutan siyasa cikin kasar.