Taurarin mata na haskawa a finafinan Hausa a Najeriya | Zamantakewa | DW | 11.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Taurarin mata na haskawa a finafinan Hausa a Najeriya

A arewacin Najeriya an fara samun karuwar mata da suka rungumi wasan kwaikwayo a matsayin sana'a a finafinan Hausa, lamarin da ke taimaka wa masana'antar Kannywood wajen samun ci-gaba.

A Najeriya sannu a hankali mata na shiga finafinan zamani na Hausa da wasannin barkwanci ana damawa da su dan inganta harkar sana’ar daga yankin arewacin kasar ko kuma dan rufa wa kansu asiri. Lamarin kuma da ya janyo karuwar mata masu zurfin ilimi da sabbin hikimomi da dabaru zuwa ma’aikatar shirya finafinan Hausa dan kara daga dajarar sana'ar a duniya. 

Maryam Habila wanda aka fi sani da suna Sparking Maryam daya daga cikin fitattun 'yan wasan Kannywood a Najeriya, ta bayyana cewa bayyana cewa a shekarun baya an fuskanci karancin mata saboda wasu matsaloli da suka jibanci addinai da kabilanci da wasu a'ladun gargajiya wadanda suka taimaka ainun wajan dakushe kwarin gwiwar mata wajan shiga harkokin finafinan zamani. Sai dai kuma Maryam ta ce an sami sauyi sosai a fannin shigar matan harakokin finafinan zamani saboda irin wayewar kai da kuma ci-gaban da aka samu. Kazalika ta ce shigar mata harkar film ya kawo gagarumar gudanmawa wajan bunkasar daukacin harkokin da suka shafi masana’antar shirya finafinan Hausa.

A shekarun baya dai an fuskanci karancin shigowar mata wajan harkar finafinan Turanci da na Hausa da ma zuwa kasashen waje wajan shirya wani fim da gogaggun ‘yan wasan kasashen ketare saboda wasu matsaloli. Amma yanzu sune ke a kan gaba, inda kuma suke taka mihinmiyar rawa wajan ilmantar da al'umma kan zamantakewa da gyara tarbiya.

Zainab Gambo Hayin Bakin Kaduna ita ma dai wata jaruma ce a bangaen shirya finafinan Hausa da wasannin barkwanci a Kannywood Najeriya ta ce yanzu abun na da ban sha’awa ba kamar yadda ake gudanar da shi a skerun baya ba. Ta ce a wasu shekarun da suka gabata, jama’ar gari da dama na da gurguwar fahimta a kan shigar mata harkar finafinai, amma a yanzu an sami sauyi sosai a cikin dukkanin tsare-tsare da sauran harkokin da suka jibanci bunkasa sana'ar. Jarumar ta nunar da cewa su da kansu na ba da tasu gudunmawar wajan inganta dukkanin shirye-shiryen finafinan.

Alhaji Suleman wanda aka fi sani da suna Justice a ma’aikatar shirya finafinan Hausa kannywood ya tabbatar da cewa mata na matukar yin tasiri a yanzu wajen inganta harkokin shirya finafinan Hausa. Sannan ya kara da cewa akwai mata da ta wannan sana’ar ce suke rufa wa kansu asiri da kuma kokarin zama abun da suke san zama a duniya ba tare da dogaro ba daga hannun samarinsu. Daga karshe dai ya nunar da cewa kashi 75 daga cikin 100 na mata sun shigo cikin fina-finan Hausa ne domin ba da tasu gudunmawarsu ga ingantar masana’antar, sanannan kuma kashi 25 zuwa 35 daga cikin dari sun dauki abun ne a matsayin sana’a.
 
Sai dai duk da rawar da mata jaruman ke takawa a cikin harkar shirya finafinan Hausa, kwararrun masana a bangaren al'adun gargajiya na janyo hankalinsu a kan sanya situra masu daraja ,da kuma kauce wa wasu dabi’un da suka saba wa al'adun daukacin al'ummomin arewacin Najeriya.