Tattaunawar sulhu da Taliban | Labarai | DW | 08.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tattaunawar sulhu da Taliban

Gwamnatin Afghanistan ta na neman sulhuntawa da kungiyar Taliban domin rage yawan hare-hare a kasar da ma yakin da aka dauki shekaru ana yi.

Shugaba Ashraf Ghani ya tura wata tawaga zuwa Pakistan, wadda ta gana da wakilan Taliban, wannan ne karon farko da shugaban ya fito ya fili ya bayyana yunkurinsa tattaunawa a hukumance da 'yan tawayen da ke neman kifar da gwamnatin kabul. A yanzu haka dai tawagar ta tattauna da kungiyar kuma har sun amince su sake ganawa.

Wannan yunkuri na neman kawo karshen yakin da ya kai tsawon shekaru 13 yanzu, ya zo ne jim kadan bayan da wasu masu kunar bakin wake suka kai hari kan ayarin motocin dakarun ketare a cikin birnin Kabul, da kuma babban ofishin hukumar leken asirin kasar. Wannan ganawa dai, wata kila ta kasanace matakin farko na kaddamar da shirin sulhu da kungiyar wadda aka kwace mulki a hannunta lokacin wani harin da aka kai mata a kabul a karkashin jagorancin dakarun Amirka a shekara ta 2001.