Tattaunawa kan rikicin Taliban | Labarai | DW | 27.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tattaunawa kan rikicin Taliban

An shiga rana ta biyu ta tattaunawar da mahukuntan Afghanistan da takwarorinsu na Pakistan ke yi game da kokarin da suke kan warware rikicin Taliban.

Pakistani Prime Minister Nawaz Sharif (R) shakes hands with Afghan President Hamid Karzai at The Prime Ministers House in Islamabad on August 26, 2013. Karzai asked Pakistan on August 26 to help arrange peace talks between his government and the Taliban, and demanded a joint campaign against extremism in both countries. The visit marks Karzai's first talks with newly elected Prime Minister Nawaz Sharif despite a history of stormy relations that have hampered efforts to end 12 years of war in Afghanistan. AFP PHOTO/ AAMIR QURESHI (Photo credit should read AAMIR QURESHI/AFP/Getty Images)

Pakistan Islamabad Nawas Sharif und Hamid Karsai Afghanistan Treffen Politik

A yau Talata ce shugaba Hamid Karzai na Afghanistan da Firaministan Pakistan Nawaz Sharif za su cigaba da ganawa a rana ta biyu kan lalaubo bakin zaren waware rikicin 'yan kungiyar nan ta Taliban da ke gwagwarmaya da makamai.

A jiya ne dai shugaba Karzai ya fara tattaunawa da Firaministan Pakistan din a Islamabad inda ya bukace shi da ya agaza masa wajen ganin an kawo karshen tada kayar bayan da 'yan Taliban din ke yi musamman ma dai ta hanyar jawo su kan teburin sulhu da gwamnatinsa.

To sai masu sharhi kan lamuran tsaro a yankin na ganin cewar abu ne mai wuya Pakistan ta iya taka wata rawa ta a zo a gani game da kashe wutar rikicin saboda ana zargin wasu 'yan kasar da taimakawa 'yan Taliban din da kudi da ma maboya a gwagwarmayar da suke yi, yayin da shi kuma Firaministan Pakistan din ya bada tabbacin kaiwa ga ci.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammed Awal Balarabe