Shugaban rundunar sojojin Najeriya Christopher Musa ya bayyana anniyar aiki tare da gwamnatin sojan Nijar, bayan da bangarorin biyu suka yi wa juna barazana sakamakon ballewa daga kungiyar ECOWAS ko CEDEAO da Nijar din ta yi jim kadan bayan sojoji sun kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.