Tattauna matsalolin arewacin Najeriya | Siyasa | DW | 12.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tattauna matsalolin arewacin Najeriya

Gwamnonin jihohin arewacin Najeriya 19 sun dukufa wajen lalibo hanyoyin magance matsalolin zamantakewa da na tsaro da jihohinsu ke fuskanta.

Alhaji Kashim Shettima

Alhaji Kashim Shettima shugaban kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya

Gwamnonin Jihohin arewacin Najeriya 19 sun gudanar da taro a birnin Kaduna domin nazarin hanyoyin shawo kan matsalolin rayuwa da na tsaro da jihohin yankin suke fuskanta sanadiyyar ringingimu na siyasa, da kabilanci da na addini dama ayyukan kungiyoyin masu tayar da kayar baya irinsu Boko Haram.

Gwamnan Jihar Filato Salamon Lalong ya bayyana gamsuwarsa da wannan taro yana mai cewa.

"Wannan taro na 'yan arewa abu ne mai mahimmanci domin dama ni tun yaushe nake hankoran ganin an gudanar da shi. Dama a baya mun fara wannan zama. Yanzu mun sake dawowa domin hadin kai da nazarin abubuwan da jihohinmu suke bukata gwamnatin tarayya ta taimaka masu da su musamman abin da ya shafi tallafa wa matasa da mata domin su samu jari. Mu a jihar Filato mun zo ne lokacin da ke da akwai basussuka da kasa biyan ma'aikata. Yanzu mun dauki matakin biyan ma'aikata. Dan haka mu yanzu a Jihar Filato matsalar kabilanci da banbance -banbance mun bata baya"

Tuni kuma jama'ar arewacin tarayyar ta Najeriya suka tofa albarkacin bakinsu a kan wannan taro na gwamnonin jihohin arewa dama abin da suke jira daga garesu. Sun yi kira ga gwamnonin da su yi aiki da matakkan da taron nasu zai dauka ,kar ya kasance na shan shayi kawai a watse. Sun kuma bayyana fatan ganin gwamnonin wannan zamanin ba za su yi irin na shekarun baya ba wadanda suka kwashe shekaru suna milki ba tare da kula da matsalolin al'umma ba.

Sai dai wani abin lura a nan shi ne wasu daga cikin gwamnonin jihohin arewacin Najeriyar ba su halarci wannan taro ba. Abin da ke nuni da irin girman matsalar rarrabuwar kawunan dake da akwai a tsakaninsu. Matsalar da 'yan kasar ke ganin ita ce dalilin kasa shawo kan matsalolin tsaro da na talauci da yankin arewacin Najeriyar ke fuskanta shekaru da dama.

Sauti da bidiyo akan labarin