Tattalin arzikin Najeriya ya kara ja baya | Siyasa | DW | 31.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tattalin arzikin Najeriya ya kara ja baya

Wani saban rahoto da aka wallafa kan sabbin alkalumman tattalin arzikin Najeriya ya nunar da cewa tattalin arzikin kasar ya yi lalacewar da babu irinta cikin kusan shekaru 30 na bayan nan.

Wani saban rahoto da aka wallafa kan sabbin alkalumman tattalin arzikin Najeriya ya nunar da cewa tattalin arzikin kasar ya yi lalacewar da babu irinta cikin kusan shekaru 30 na bayan nan. Amma kuma gwamnatin kasar ta ce har yanzu tana hango haske ga makomar kasar a nan gaba.

Duk da cewar dai an bude babi na shekarar bana a cikin halin wai wai, kadan na 'yan kasar ne dai su ka yi tsammanin girman matsala ga tattalin arzikin kasar da ke tangal-tangal. To sai dai kuma wani rahoton zango na biyu na hukumar kiddidigar kasar dai ya ce tayi baki ta kuma kara lalacewa ga tattalin arzikin da a zango na biyu ya samu gibin da ya kai na kaso 2,06 cikin dari a wattani ukun kacal. Matsayin kuma da ya tabbatar da masassarar banan kuma ya kara jefa 'yan mulkin na Abuja zuwa ga kari na matsin lamba.

Kara rushewar lamuran dai ta dauki hankalin majalisar zartarwar kasar da ta zauna a Abuja ta kuma ce karin hakuri na zama na wajibi bisa manufofin da take dauka domin fitar da kasar daga dogaro da harkar man fetur. Kemi Adeosun dai na zaman ministar kudin kasar kuma jagora ga tattalin arzikin da ke cikin ni 'yasu a yanzu.

"Muna inda muke ne saboda hankalinmu ya koma hakar man sannan da kashe kudin ga harkoki na yau da na kullum ba mu zuba jari. Kiddidigar ta yau na nuna mana karara cewar yawan jarinmu na ta karuwa, muna sauyin akalla daga sharholiya zuwa in da ya dace. In ka gina hanya tana nan har shekaru 40 , layin dogon da muke son gyarawa na nan tun daga mulki na mallaka, dole ne mu sa jari ga aiyyukan raya kasa wannan ita ce dabara ta wannan gwamnatin, ba mu rude ba duk da lokaci ne na rudani, muna nan kan hanya, in zamu kara hakuri kadan mu fito daga wannan yanayi mai wahala, Najeriya za ta ga amfanin.Kuma duk masu sukar tamu ba wanda ya zo ya ce mana ga mafita sai dai a ce ba mu son abun da yake faruwa. Ko da kuwa ba ku son abun da yake faruwa dole ku ganshi, saboda in har za mu dora hankalinmu a kan man fetur, kuma farashin man fetur zai yi kasa, sannan yawan wanda muke haka zai ragu to dole mu ji a jiki, saboda haka dole ne mu gina tattalin arzikin da babu mai a cikinsa."

To sai dai kuma koma ya zuwa ina hakuri na 'yan kasar ke iya kaiwa dai, ya zuwa yanzu hankali na tashe da 'yan kasar da suka ce sai sauyi amma kuma suka kalli rayuwarsu na sauyawa ya zuwa wahala. An kare zangon na biyu dai tare da hauhawar farashin da ya kai sama da kaso 17 cikin dari, adadi mafi yawa a shekaru sama da 11, sannan kuma da raguwa na ayyukan yi da kara rushewar darajar kudin kasar na Naira.

To sai dai kuma a fadar hajiya Zainab Shamsuna Ahmed da ke zaman karamar ministar kasafin kudin kasar sannan kuma mai lura da hukumar kiddidigar, shi kansa rahoton na nuna alamar sauyin da ke shirin amfanar kasar a kankane na lokaci.

Hukumar lamuni ta IMF dai ta yi hasashen yiwuwar shiga massasarar da ta kai ta kaso 1,8 a karshe na shekarar a yayin kuma da Abujar ke fadin za ta fara nuna alamun kyau tun daga zango na uku dama na hudun da ke iya warke komai.

Sauti da bidiyo akan labarin