1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a fuskanci karancin magunguna saboda yakin Iran

Muhammad Bello AH
March 19, 2026

Masu ruwa da tsaki a harkar hada magunguna ,sun bayyana fargaban cewar muddin ba a samu saukin rikicin gabas ta tsakiya ba, hakan ka iya haifar da yankewar magungunan

https://p.dw.com/p/5AjLc
Hoto: Peter Kovalev/TASS/dpa/picture alliance

Yawancin magungunan,sun hada da wadanda ke  shigowa daga nahiyoyin Turai da Asiya.

Kapsel Pille Symbolbild
Hoto: Andrea Danti/Zoonar/picture alliance

Sama da kaso 70 cikin dari dai na  magungunan da ake amfani da su a cikin Najeriya, daga musamman kasashen India da Chaina ake shigo da su ,inji hukumomi.

mRNA Impstoff / Symbolfoto Impfung
Hoto: Steven Heap/Zoonar/picture alliance

Rurewar yakin dai na Gabas ta Tsakiya,an tabbatar zai shafi samarda kudaden tallafi kan wasu cututtuka da gwamnatin tarayyar Najeriya ke yi, kamar su cutar karya garkuwar jiki ta Hiv da tarin fuka,da Malaria da musamman harkokin kula da lafiyar mata.

Chromosomen
Hoto: Ersin Arslan/Zoonar/picture alliance

Katse safarar Danyan mai daga yankin Gabas ta Tsakiya,da dode turbar Hormuz, fargabar samun tsaiko a hada-hadar ta magunguna an nunar ta bayyana a kasashen yamma.

Symbolbild Impfung
Hoto: Olena Mykhaylova/Zoonar/picture alliance