1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Tasirin wakokin Rap a tsakanin Matasa

Abdul-raheem Hassan
February 23, 2018

Mawakan Hip-Hop Rap ko Gambara a Najeriya, sun sha alwashin inganta salon wakokin ta yadda za su farfado da al'adun gargajiya a tsakanin matasa.

https://p.dw.com/p/2tELF

A kasar Uganda matasa masu rawar lankwansa ko Break Dance, Sama da matasa 20 daga kasashen Uganda da Ruwanda da kuma Kenya sun fafata a da salon rawa kala-kala, inda aka zabi gwani don samun kyaututtuka masu tasiri. 

A stakanin shekarun 1970 ne aka kirkiro da salon rawar Lankwasa wato Breakdance, rawar da yawanci mawakan Rap ke amfani da shi.

A Najeriya ana zargin mawakan Hip-Hip Rap da kalaman batanci ko zagi a wakokinsu, amma yanzu sun ce za su nade kafar wando wajen sanya kalaman hausa da al'adun malam Bahaushe wajen ganin sun raya al'adun gargajiya tsakanin matasan kasar. Tare da fadakar da matasa illolin shaye-shaye da neman sana'a domin dogaro da kai.