1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kason kananan hukumomi kai tsaye

Abdullahi Tanko Bala
June 20, 2019

A Najeriya matakin gwamnatin tarayyar kasar na bai wa kananan hukumomi kudadensu kai tsaye zai rage matsalolin talauci da tsaro da bunkasa cigaba a yankunan

https://p.dw.com/p/3Kmvr
190620 Karikatur: Kommunen Finanzen
Hoto: Abdulkareem Baba Aminu

A karon farko bayan shekaru fiye da goma kanana hukumomi 774 na Najeriya sun samu kudaddensu kai tsaye daga asususn gwamnatin tarayya a mataki da ke nuna baiwa kananan hukumomin yancin gudanar da kudaden.

Turawa kananan hukumomin kudadensu kai tsaye ya biyo bayan dokar da hukumar sa ido  kan kudadde ta Najeriya ta yi ne wanda ya kawo karshen asusun hadin gwiwa tsakanin kananan hukumomi da gwamnatocin jihohi da tun 2003 da aka bulo da ita. Masana da masharhanta dai sun sha sukar asusun hadin gwiwa tsakanin kananan hukumomi da gwamnatocin jihohi mataki da suka ce ya talauta kanana hukumomin, tare da mayar da su ‘yan amshi shatan gwanoni.