1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasiri da raunin AU a Afirka a shekaru 60

Abdullahi Tanko Bala LMJ
May 26, 2023

Takaddamar siyasa da rikicin kabilanci a Afirka, na cikin nakasun kungiyar AU da ke hana Afirka more arzikin nahiyar. Amma wasu kasashe na yunkurin fara hana kasashen waje kwashe ma'adinai.

https://p.dw.com/p/4RrUt
Habasha | Shekaru 60 | AU
Bikin cikar kungiyar AU shekaru 60 da kafuwaHoto: Solomon Muchie/DW

A sharhinta jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi nazari kan cikar kungiyar Tarayyar Afirka shekaru 60 da kafuwa, tare da taken: "Magance matsalolin Afirka." Jaridar ta ce shekaru 60 da suka wuce aka kafa kungiyar hadin kan Afirka OAU a birnin Addis Ababa tare da fata da buri mai yawa. Ya kamata kungiyar AU ta wuce matsayin sauyin suna kawai daga tsohuwar kungiyar OAU zuwa AU. Bikin kafa kungiyar OAU ya gudana ne a ranar 25 ga watan Mayu 1963 kuma har ya zuwa wannan lokaci ana bikin wannan rana a matsayin ranar duniya ta Afirka. Wannan bai da wata dangantaka da nasarorin da kungiyar ta samu a tsakanin kasashe mambobinta, sai dai dagowar da ta yi daga karshen mulkin mallaka a Afirka da abin da ya biyo baya na karsashi da kwarin gwiwa.

OAU ta kasance kungiya ta kasashen Afirka da suka sami 'yanci, inda ta hada kan kasashen domin samun matsayi da martaba a idanun duniya tare da sasanta rikice-rikice da wanzar da zaman lafiya da samar da kyakkyawan yanayin rayuwa ga al'ummar nahiyar. An yi nasarar cimma wannan a matakin farko to sai dai matsalolin da suka sa aka kirkiri kungiyar AU har yanzu suna nan shekaru 60 bayan kafuwarta. Ko da yake Yan kadan daga cikinsu ana iya dabbaka su, sai dai rashin  rundunar tsaro na kanta, da manufar mambobin kasashen kungiyar na kau da kai da kin sanya baki a al'amuran cikin gida na wata kasa daga cikinsu ba, ya raunana martabar kungiyar. A saboda haka kungiyar ba ta damu da gwamnatoci da ke mulkin kama karya ba, kamar gwamnatin Idi Amin na Uganda. Hasali ma a shekarar 1975 shugabannin kasashen suka zabi Idi Amin a matsayin shugaban kungiyar OAU, ba tare da la'akari da martabar kungiyar ba.

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango | Ma'adinai
Aikin hakar ma'adinai a Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Getty Images/P. Pettersson

"Idan ka ba ni zan karba" shi ne taken sharhin Jaridar die tageszeitung. Jaridar ta yi tsokaci a kan yadda Chaina ta ke tatsar albarkatun kasa a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Jaridar ta ce shekaru 15 da suka wuce tsohon shugaban kasar Kwango Joseph Kabila ya sayar da wasu yankunan ma'adanai masu daraja ga kasar Chaina, amma a yanzu shugaba Félix Tshisekedi wanda ya gaje shi yana son warware wannan ciniki. Abin da zai biyo bayan wannan dambarwa dai, yana da matukar muhimmanci ga duniya. Tshisekedi zai tado da batun a ziyarar da zai kai Chaina. Kaso 70 cikin 100 na ma'adanin cobalt ana samunsa ne a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, kuma kaso 80 cikin 100 ana fidda su ne zuwa chaina. Kamfanonin Chaina dai su ne suka mamaye fannin hakar ma'adanin colbalt a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da kuma samar da shi a duniya, ma'adanin da idan babu shi, ba za a sami dorewar makamashi ba a duniya. A taron tattalin arzikin duniya da ya gudana Davos a watan Janairun 2023, Shugaba Tshisekedi ya ce ya zama wajibi a sake bitar yarjejeniyar. Tunin dai majalisar dokokin kasar ta kada kuri'ar amincewa da sake tattauna yarjejeniyar da gwamnatin baya ta cimma da Chaina.

Sudan | Rikici | Gudun Hijira
Al'ummar Sudan na ci gaba da zama cikin halin taskuHoto: Amanuel Sileshi/AFP

Jaridar die tageszeitung din ta kuma tabo batun Sudan wadda ta bayyana a wani sharhin mai taken: "Kasar da aka lalata." Jaridar ta ce yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma ba ta aiki kuma babu wani haske da jama'a suke gani na ci gaba. Jaridar ta ce Sudan na cikin wani hali na bukatar taimakon jin-kai ga al'umma. Sai dai kungiyoyin agaji sun koka da cewa lamarin na da matukar hadari isa ga rumbunansu da ke Port Sudan yayin da ake kokarin kai kayan agaji zuwa Khartoum babban birnin kasar. Fada tsakanin sojojin gwamnati da kungiyar sa-kai ta RSF, na ci gaba da dauki ba-dadi duk da yarjejeniyar tsagaita wuta na kwanaki bakwai. Kasashen da suka shiga tsakani Amurka da Saudiyya sun gargadi kungiyoyin biyu su kiyaye. Majalisar Dinkin Duniya ta ce a halin yanzu mutane miliyan 25 daga cikin 'yan Sudan miliyan 45 na bukatar taimakon jin-kai. Majalisar Dinkin Duniyar ta ce akwai mutane miliyan daya da suka tagayyara a cikin gida tun bayan barkewar rikicin, yayin da wasu mutanen dubu 319 suke gudun hijira a makwabtan kasashe.