Tashin hankali a yajin aikin gama gari a Faransa | Labarai | DW | 18.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashin hankali a yajin aikin gama gari a Faransa

Yajin aiki da zanga-zanga sun janyo tsaiko a faɗin ƙasar Faransa

default

Matasa sun shiga jerin masu zanga-zangar gama gari a Faransa

Yajin aikin da ake yi a Faransa ya rikiɗe zuwa tashe tashen hankula a yau Litinin yayin da ɗaliban sakandare suka bi sahun direbobin jiragen ƙasa da na manyan motoci wajen gudanar da zanga-zangar nuna adawa da shirin shugaba Nikolas Sarkozy na yiwa tsarin fansho kaskwarima. 'Yan sanda sun ce matasa a faɗin ƙasar baki ɗaya sun yi ta bankawa motoci wuta sannan a wasu garuruwan sun yi ta jifa da bama-baman fetir da duwatsu. Yajin aikin ma'aikatan jirgin ƙasa da toshe hanyoyi da direbobin manyan motoci ke yi, ya gurgunta tsarin sufurin ƙasar. Yajin makon guda a matatun mai ya tilasta sama da gidajen mai dubu ɗaya rufewa saboda ƙarancin mai yayin da jami'an sufurin jiragen sama suka ɗauki matakan soke tashi da saukar sama da kashi 50 cikin 100 na jiragen sama a ƙasar. Shirin yiwa tsarin fansho kwaskwarima dai zai ƙara yawan shekarun zuwa fansho daga 60 zuwa 62. A gobe Talata an shirya gagarumin jerin gwano na ƙasa baki ɗaya, kwana guda gabanin wani zaman majalisar dattawa, inda ake sa rai za ta amince da sabon tsarin.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Halima Balaraba Abbas