Tashin hankali a ƙasar Gini | Labarai | DW | 17.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashin hankali a ƙasar Gini

Ana zaman dar-dar a ƙasar Gini, bayan karawar jami'an tsaro da masu bore.

default

'Yan sandan ƙasar Gini suka kama wani, mai zanga-zanga.

Ana ci gaba da zama cikin zullumi a ƙasar Gini Konakry a inin yau, bayan da jami'an tsaro suka farwa masu zanga-zanga a jiya, abinda ya kai ga mutuwa mutane biyu. Masu zanga-zangar dai magoya bayan Cellu Dalle Jalo ne, waɗanda suka yi zargin an tabka magudi a zaɓen. Baƙi masu sa ido a zaɓen, galibinsu sun yi Allah wadai da yadda jami'an tsaro suka yi aiki da ƙarfi wajen farma masu zanga-zangar, inda izuwa yanzu jami'anro suka kashe mutane huɗu, yayin da suka kama wasu da dama. Shi dai Jalo wanda shine ya zo na gaba a zagayen farko na zaɓen, ya kai ƙara a kotun ƙolin ƙasar, inda ya nemi da ta ƙwato masa haƙƙin sa. Inda yace an kada shi ne kawai bayan tabka magudi. Kana Cello Dalle Jalo, ya yi Allah wadai da yadda jami'an tsaro ke cin mutunci magoya bayansa wadanda aksari Fulani ne. Jalo ya shaida wa gidan radiyon Faransa na RFI cewa, bayan kiran da ya yi na a zauna lafiya, amma jami'an tsaro sunci gaba da farma 'yan ƙabilarsa ta Fulani, inda izuwa yanzu aka tsare magoya bayan nasa dayawa a kurkuku.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu