Tashin bama-bamai a Iraƙi | Labarai | DW | 17.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashin bama-bamai a Iraƙi

Wasu motoci biyu maƙare da bama-bamai sun tarwatse a Bagadaza babban birnin ƙasar Iraƙi tare da hallaka mutane 12 da kuma jikkata wasu 29.

Rahotanni sun bayyana cewar ɗaya daga cikin motocin ta tarwatse ne a wata hanye mai cike da hada-hadar kasuwanci da ke Mashtal a yankin gabashin Bagadaza, yayin da dayar kuma ta tarwatse a makamanciyar wannan hanya da ke garin Amriyah a yammacin Bagadazan. Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin harin, sai dai dama a 'yan makwannin baya-bayan nan ƙungiyar 'yan ta'addan IS da ta addabi ƙasashen Irakin da Siriya ta dauki alhakin wasu jerin hare-hare da aka kai a Bagadazan.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman