Taron warware rikicin Siriya a Jamus | Siyasa | DW | 12.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron warware rikicin Siriya a Jamus

Ministocin tsaro da na harkokin wajen na kasashe daban-daban sun yi musayar yawu a wani taro a birnin Munich na Jamus don kawo karshen rikicin da ma tada kayar bayan 'yan IS.

Shi dai wannan taro na birnin na Munich ya samu halartar ministocin harkokin tsaron kasashen Iraki da Jordan da Saudiyya gami da China. Har wa yau sakataran harkokin tsaron Amirka da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da sakataren harkokin wajen Amirka gami da shugaban NATO sun bakunci zauren taron.

Syrien Aleppo Zerstörung Bombardierung

Taron Munich na kokarin warware rikicin Siriya.

Da ya ke tsokaci kan abinda ya tarasu, Jens Stoltenberg da ke zaman sakataren kungiyar tsaron NATO suka ya yi ga Rasha bisa irin rawar da ta ke takawa a yakin na Siriya inda ya ke cewar ''zuwa yanzu dai za mu iya cewar Rasha na kai hare-hare ne kan 'yan adawar Siriya ne ba 'yan IS ba, kana ta na kuma cigaba da kai hare-hare ta sama wanda ke dakushe yunkurin mu na samun maslaha cikin ruwan sanyi.''

Shi kuwa sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry cewa ya yi ''Rasha aiki kafada da kafa da Amirka tare da sauran kasashe. Zamu cimma nasara ga batun bayar da agaji gami da sasanta bangarorin da basa ga maciji da juna da nufin kyautata rayuwar mutanen Syriya.

Wannan kalamai da Kerry ya yi ne ma ya sanya ministan harkokin wajen China Wang Yi nuni yake dukkanin wadanda suke da ruwa da tsaki sun amince da samar da kayan tallafi ga 'yan gudun hijirar Siriya kuma mambobin kungiyar kasa da kasa da ke tallafawa Siriya za su tabbatar da ganin an cimma kudurin da aka sanya a gaba.

Sauti da bidiyo akan labarin