Taron tunawa da wanda aka kashe a Paris | Labarai | DW | 27.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron tunawa da wanda aka kashe a Paris

Kimanin mutane dubu biyu ne suka hallarci taron addu'o'i da aka yi na tunawa da wanda aka hallaka a hare-haren birnin Paris makonni biyu da suka gabata.

Shugaban Francois Hollande na Faransa din ne ya jagoranci taron a gaban wani gidan adana kayan tarihi na soji da ke tsakiyar birin Paris din, inda aka karanto sunyen mutane 130 da suka rasu a harin wanda kungiyar IS ta dauki alhakin kaiwa.

Shugaba Hollande ya ce ''ranar Juma'a 13 ga wannan watan rana ce da ba za mu taba mantawa da ita. An afkawa Faransa da yaki wanda wasu 'yan ina da kisa suka kitsa shi su daga wajen kasar.''

Yayin jawabinsa dai Hollande ya ce ko kusa Faransa ba za ta taba razana da tada kayar bayan 'yan ta'adda ba musamman ma IS kuma za ta yi bakin kokarinta wajen ganin ta dakile dukannin wani aiki na ta'addanci.

Shugabannin siyasa na kasar da jami'an diflomasiyya da kuma wasu daga cikin mutane kimanin 350 da suka jikkata yayin hare-haren na daga cikin wanda suka halarci wannan taro.