Taron sasanta kan kasa a Iraki | Labarai | DW | 16.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron sasanta kan kasa a Iraki

Prime ministan Iraki Nouri al-Maliki ya bayyana cewa,rundunar sojin kasar ta bude kofofinta wa tsoffin dakarun zamanin tsohon shugaba Sadam Hussein,wadanda suka rasa mukamansu bayan mamayen Iraki da Amurka tayiwa jagoranci.Kazalika Maliki ya kuma mika goron gayyata wa membobin jammiyar Baath ta sadam,musamman wadanda baa samesu da laifukan da suka sabawa kasa ba.Wadannan kalamai nasa sunzo ne adaidai lokacin da gwamnatin Irakin ta kaddamar da taron sasanta kann kasa,dake da nufin yakar rikice rikice na kabilanci da addini dake gudana a kasar.Yan siyasa daga darikun Shia da Sunni da Kurdawa ne ke halartan taron.To sai dai rahotanni daga Irakin na nuni dacewa masu tsattsauran raayi na shia da Sunni sunkib halartan taron.