Taron neman shawo kan rikici wasu kasashe | Siyasa | DW | 27.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron neman shawo kan rikici wasu kasashe

kammala taron da ake yi a birnin Luanda na Angola na kasashen yankin Grands Lacs wanda kungiyar kasahen tare da hadin gwiwar tarrayar Afirka da MDD suka shirya domin warware rigingimun siyasa da ake fama.

A cikin wata sanarwa ta karshe da shugabannin kasashen Yankin na Grands Lac da na SDAC suka saka hannu a kai  sun yi Allah wadai da tashe-tashen hankula da aka yi fama da su a ranaku 19 da 20 ga wannan wata a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango tare da yin kira ga dukkanin bangarorin da ke yin jayyaya a kan mulkin da su samar da sulhu cikin ruwan sanyi domin kawo karshen rikicin siyasar kasar.Kasashen da ake neman sassanta rikici sun hada da Sudan ta Kudu, da Burundi, da Kwango Brazaville da kuma Jamhuriyar demokaradiyyar kwango.Shugabannin kasashen yankin na Grand Lac sun kuma bukaci da a kwance damara mayakan da suka dauki makamai a Kwango inda aka cimma wata yarjejeniya tsakanin rundunar sojojin Kwango da MONUSCO don ci gaba da yin farautar masu dauke da makamai a yankin arewacin Kivu da ke a gabashin Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango.

Taron wanda aka kammala ya samu halartar masu shiga tsakanin na Kungiyar Tarayyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya da kuma wasu shugabannnin kasashen a ciki har da na Chadi Idriss Deby wanda ke rike da matsayin shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka da na Kwango Brazzaville da Zambiya ya tanadi bin sau da kafa irin abubuwan da aka tsaida.Wani abin lura dai shi ne cewar daga cikin shugabanni 13 na kasashen na Yankin Grands Lacs hudu kawai suka halarci taron abin da ya sa ake ganin zai iya zama sanadiyyar tashin liki a gaba domin kuwa wasu daga cikin shugabanin kamar na Burundi da Sudan ta Kudu wadanda kasashensu ke fama da tashin hankali na siyasa sun kaurace.

Sauti da bidiyo akan labarin