Taron Musulunci da zaman lafiya | Siyasa | DW | 29.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron Musulunci da zaman lafiya

"Muna bukatar cibiyoyi na addini da zasu rika bibiyar abin da ake koyarwa na addinin Musulinci.Me ake koyarwa, waye ke koyarwar, sannan a samar da wasu da zasu rika sanya idanu".

Islam Konferenz Gipfel in Dakar

Mahalarta taron Musulinci da zaman lafiya

A ranar Talatan nan ce aka kammala wani taron kasa da kasa a kan Musulinci da zaman lafiya. Taron da aka yi a birnin Dakhar na kasar Senegal ya tattara shugabanni na addinin Islama 'yan fafutikar kare hakkin bil Adama da 'yan siyasa wadanda suka tattaru daga kasashe daban-daban na duniya dan tattauna batun kakkausan kishi na addini da ayyukan ta'addanci da irin rawar da addinin Islama ke takawa wajen samar da ci gaba.

Babban burin taron dai shi ne ganin an lalubo hanyoyi da za a sami zaman lafiya a duniya sannan aga wace rawa ce mata da matasa zasu taka wajen ganin an tabbatar da ganin dorewar zaman lafiya aga rawar da kowane rukunin al'umma zai taka wajen ganin an samu zaman lafiya..

Har ila yau taron nada burin ganin an kawar da yadda ake ganin addinin Islam a matsayin wani addinin da ke da alaka da tashin hankali sabanin sunansa na asali wato addinin zaman lafiya da karramawa.

To ko malaman na addinin Islama nada rawar da zasu taka wajen fahimtar da menene ma addinin na Islama Dr. Ibrahim Ahmad Muqary Zariya shi ne limami a babban masallacin Abuja Najeriya.

" Tabbas malamai na ainihi nada rawar da zasu taka saboda ma nuna halin ko'inkula da ake musu shi yasa ma yanzu ake ganin abin da ke faruwa, wasu da basu cancanci koyar da addini ba sun shi rigunan malamai wasu 'yan siyasa ne wasu tsaffin ma'aikatan gwamnati. Ana yi wa wa'azi karan tsaye".

Shugaban kasar Senegal Macky Sall wanda kasarsa ke da kashi 92 cikin dari na al'ummarta ke zama Musulmi da cibiyar zaman lafiya ta Medina Baye da kungiyar Jamhiyatu Ansaarud da ke a kasar ta Senegal da sarkin Moroko suka dauki nauyin tsara wannan babban taro na kasa da kasa, wanda ake ganin zai tallafa wajen ganin samar da zaman lafiya a duniya sai dai a cewar Dr. Ibrahim Ahmad Muqary irin wannan taro idan har ana so aga an cimma burinsa na ganin an samu zaman lafiya a kasashen duniya sai an tashi wajen aiwatar da abinda taron ya cimma.

"Muna bukatar cibiyoyi na addini da zasu rika bibiyar abin da ake koyarwa na addinin Musulinci. Me ake koyarwa, waye ke koyarwar, sannan a samar da wasu da zasu rika sanya idanu kan wadannan cibiyoyi, ta haka za a kawar da cusawa matasa kakkausan ra'ayi wanda ba na addinin Islama ne na hakika ba".

Shi kuwa ana nasa ra'ayin Sheikh Abdullahi Bala Lau shugaban kungiyar Izalatul Bidi'a wa ikamatussunnah na kasa a Najeriya a nasa ra'ayin ya ce daya daga cikin hanyoyi da ake ganin za a kai ga samun zaman lafiya na zama ba wa matasa da mata samun ilimi na addini na gaskiya a kan Musulunci.

"Ilimin addinin Musulunci na gaske hadi da ilimin Boko na gaskiya bisa jagorancin malamai na hakika idan aka ba wa mata da matasa a matsayinsu na jigon al'umma, hakan zai taimaka wa matasa su san addini cikin sauki amma idan har matasa zasu rika neman ilimi su kadai ba tare da malamai da suka da ceba to zasu iya zama masu tsatsauran ra'ayi da za a iya cewa masu tsatsauran ra'ayin addini akansu ba wai koyarwar Musulinci ba "

A cewar malaman dai irin wannan taro na Musulunci da zaman lafiya da Senegal ta karbi bakuncinsa da zummar warware matsaloli da ke shafar addinin duba da karuwar kungiyoyi irinsu IS al-Shabab da Boko Haram a Najeriya dole malamai su tashi dan sanar da matasa menene Musulunci ta yadda zaman lafiya zai ci gaba da dorewa tsakaninsu da wadanda ba Musulmai a dena kallon addinin da fentin da aka yi masa na ta'addanci.

Sauti da bidiyo akan labarin