1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Antonio Guterres: Bukatar gyara a duniya

September 22, 2021

Yayin da aka fara gudanar da babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 76 a birnin New York na kasar Amirka, annobar corona virus da kuma sauyin yanayi za su kasance batutuwa na gaba-gaba da za a tattauna.

https://p.dw.com/p/40fqj
NYC, UN | Vereinte Nationen | Antonio Guterres
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio GuterresHoto: Xie E/Xinhua/picture alliance

Yayin bude taron na bana, shugabannin kasashen duniya sun koka kan yadda aka sami rashin daidaito wajen samar da allurara riga-kafin annobar corona da kuma rarrabuwar kai da ya kawa cikas ga yaki da cutar a duniya. Annobar dai ta yi sanadiyyar mutuwar miliyoyin mutane, kuma har kawo yanzu ta ke ci gaba da yin barazana ga sauran rayuka. Yayin da yake jawabi a zauren majalisar, sakatare janar na majalisar Antonio Guterres ya ce duniya tana fuskantar babbar barazana da ya zama wajibi a hada karfi wajen dakile wa: "A gefe guda mun ga yadda allurar riga-kafin corona ta habaka cikin lokaci, wanda ke zama wata nasara ta kimiyya da kwarewar dan Adam. A wani gefen kuma mun ga rashin tabbas na siyasa da son kai da kuma rashin yarda. Wasu sun tsallake hadarin annobar, yayin da har yanzu wasu suke cikin hali na rashin tabbas."

Karin Bayani: Fargabar corona nau'in Delta a Najeriya

Guterres ya ce akwai bukatar kawo karshen bambance-bambance guda shida da ke tsakanin kasashen duniya da suka hada da zaman lafiya da sauyin yanayi da ratar arziki da bambancin jinsi da sadarwar zamani da kuma ratar da ke tsakanin al'umma. Shi ma dai shugaban kasar Chaina Xi Jinping ya ce duniyar a halin yanzu ta shiga cikin wani sabon rudani da kuma sauye-sauye. Shugaba Jinping ya gabatar da jerin sabbin shawarwari da dabaru kan batutuwan da suka shafi samar da hadin kai da ma farfado da tattalin arziki da bunkasa huldar kasa da kasa da kuma inganta tsarin mulkin duniya, shawarwarin da suka sami karbuwa a wajen wakilan wasu kasashen a cewar wakilin Chaina na dindindin a Majalisar Dinkin Duniyar Zhang Jun.
Yayin da kasarsa ke cikin jerin na baya-baya a riga-kafin, shugaban kasar Zambiya Hakainde Hichilema cikin rashin jin dadi ya ce akwai bukatar yin daidaito wajen samar da allurara riga-kafin annobar: "Duk da cewa mun dauki batun riga-kafin annobar corona da muhimmanci, Zambiya ta sami damar yi wa kaso uku kacal na al'ummarta riga-kafin corona wanda ya yi hannun riga da kudurin kasar na yi wa kaso 70 cikin 100 riga-kafin gabanin karshen shekara mai zuwa. Wannan ya nuna karancin alluran a kasashe masu tasowa. Mai girma shugaba yana da kyau a farfado daga barnar da annoba ta yi da kuma halin da kasashe za su shiga, idan suka kulle kofofin bunkasa tattalin arzikinsu."

NYC, UN | Vereinte Nationen | Antonio Guterres
Taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 67Hoto: Eskinder Debebe/UN Photo/Xinhua/picture alliance

Karin Bayani: Cin hanci cikin yaki da corona a Najeriya

Yayin taron dai, ana sa ran mayar da hankali kan batun sauyin yanayi da wariyar launin fata da kuma ci gaba da samun rarrabuwa kai a duniya. Wasu dai na ganin cewa da sauran runa a kaba, yayin da ake jiran martanin kwamitin duba takardu na Majalisar Dinkin Duniya da ke nazari kan wasikar da kungiyar Taliban da ke mulki a kasar Afghanistan ta aike wa majalisar kan bukatar ba ta damar yin jawabi a zauren majalisar yayin taron na bana, gwamnatin da har yanzu ake ganinta a matsayin haramtaciyya.