1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU na sake dabarun warware matsalolin tsaron Afirka

Abdul-raheem Hassan RGB
December 23, 2021

Kungiyar Tarayyar Afirka na wani zama a birnin Durban a kokarin sake dabarun warware matsalolin tsaro da suka janyo asarar miliyoyin rayuka da tilasta ma da dama yin hijira.

https://p.dw.com/p/44lpn
Flagge der Afrikanischen Union
Hoto: Klaus Steinkamp/McPHOTO/imago images

Shekaru da dama Kungiyar Tarayyar Afirka AU na kokarin warware rikici a nahiyar da yaki da rikicin siyasa ya yi sanadiyar mutuwar miliyoyin jama'a tare da tilasta da dama yin hijira. Wannan ya sa kungiyar gudaanar da zaman sake dabarun warware matsalolin a birnin Durban na Afirka ta Kudu. 

Ganawar musamman da wasu muhimman bangarorin Kungiyar Tarayyar Afirka AU, na zuwa ne a dai-dai lokacin da wasu kasashe a nahiyar kamar Habasha da Sudan ta Kudu ke fuskantar rikicin da ke janyo zubar da jini, a yayin da Mali da Gini da wasu kasashen Afirka kuma ke fama da rikicin siyasa uwa uba wasu kasashen yankin Sahle na cikin tsaya mai wuya a sakamakon hare-haren  'yan ta'adda. Shugaban cibiyar warware takaddama a nahiyar Afirka.

Karin Bayani: AU ta nemi a hau teburin sulhu

A shekarar 2003, AU ta kirkiro da tsarin APRM shirin da ke bita kan ci gaban kyakyawar shugabanci a kasashen Afirka, da kuma hango alamun tashe-tashen hankula. Yanzu haka, an dan samun hadin gwiwa tsakanin APRM da kwamitin sulhu na tarayyar Afirka, don tabbatar da tsari mai kyau na warware rigingimun ta'addanci a nahiyar.

Amma masana na ganin lokaci na kurewa nahiyar Afirka na samar dama warware rikicin da ake fama da kuma hana sabbin tashe-tashen hankula bulla. Wannan ya sa Gounden ke ganin akwai bukatar jan hankalin shugabannin nahiyar cikin gaggawa.

Ana fatan gabatar da dukannin kudurorin da aka cimma a ganawar birnin Durban, ga uwar kungiyar ta AU don duba yiyuwar tabbatar da shi nan gaba, matakan da ake sa ran cimma a taron zai taimaka wa kasashe zuwa mataki na gaba.