Najeriya: AU ta nemi a hau teburin sulhu | Labarai | DW | 22.10.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: AU ta nemi a hau teburin sulhu

Kungiyar Tarayyar Afirka ta nemi a gaggauta daukar matakin magance rikicin da ya balle a sakamakon zanga-zangar ENDSARS. A sanarwar da ta fitar a wannan Alhamis ta yi alla-wadai da rikicin da ya janyo asarar rayuka.


Kungiyar tarayyar Afrika ta AU ta yi alla-wadai da rikicin da ya barke a yayin zanga-zangar ENDSARS a Najeriya. Shugaban kungiyar Moussa Faki Mahamat  ya yi kira da a dauki matakin maslaha wajen warware rikicin. Ita ma Kungiyar ECowas ta gargadi jami'an tsaron Najeriya a game da amfani da karfin da ya wuce kima kan masu zanga-zangar. 


Hankula na tashe a jihohin da ake gudanar da wadannan zanga-zangar musanman a birnin Legas inda mutum sama da goma suka mutu a harbe-harben sojoji. Gwamnatin kasar dai ba ta kai ga cewa komai kan asarar rayukan da ake cewa an samu ba. Rikicin Legas ya dauki sabon salo na kone-kone da lalata kayayyaki bayan kashe-kashen na ranar Talatar da ta gabata.