1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kafa gwamnatin rikon kwarya a Mali

Abdourahamane Hassane LMJ
August 19, 2020

Sojojin da suka karbi mulki a Mali, sun sha alwashin kafa gwamnatin rikon kwarya, da za ta tabbatar da ganin an gudanar da zabubbuka domin sake mayar da kasar bisa tafarkin dimukuradiyya.

https://p.dw.com/p/3hCbM
Mali I  Demonstration gegen Regionalblock ECOWAS in Bamako
Sojoji sun kwace mulki a MaliHoto: Reuters/M. Kalapo

Ko da yake dai, al'ummar kasar MAlin na maraba da matakin da sojojin kasar suka dauka, amma kungiyoyi da hukumomin na duniya da dama, na ci gaba nuna rashin amincewarsu. Tuni dai kungiyar ECOWAS ta yi barazanar tura rundunarta domin rufe iyakokin kasar baya ga kakaba mata takunkumi, idan har ba a mayar da shugaban bisa kujerarsa ba. Tuni dai kungiyar Tarayyar Afirka AU, ta sanar da cewa dakatar da Malin daga cikinta. An dai kwashe kusan sa'o'i uku a cikin daren Laraba, kafin Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta mai lakabin IBK ya amince ya yi marabus, biyo bayan boren sojojin da ya rikide ya zuwa juyin mulki.

Rücktrittserklärung von Malis Präsident Boubacar Keita auf ORTM
Hambararren shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar KeitaHoto: ORTM/Reuters

A karshe shugaban ya amince ya sauka daga mukaminsa duk da irin gargadin da kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO ta yi, kan cewa za ta saka wa kasar takunkunmin karya tattalin arziki, tare da tura rundunar sojojin kungiyar domin mayar da shi kan madafun iko. IBK ya ce ya gwamace ganin ba a zubar da jini ba a kasarsa: "Ya ku 'yan kasata 'yan Mali. Ba ni da wani zabi illa bayar da kai bori ya hau; saboda ba na fatan ganin an zubar da jini a kasata domin na tsaya kan mulki don haka na yanke shawarar na yi murabus.''

Sojojin wadanda suka kifar da mulkin a karkashin jagorancin Kanal Sadio Camara duk da cewar har yanzu ba a tantance wanene jagoran juyin mulkin ba, na zargin gwamnatin Mali da gazawa wajen magance matsalolin kasar na cin hancin da karbar rashawa da rashin adalci a shari'a, sannan ga rikicin siyasa da na 'yan ta'adda da ya addabi kasar tsawon shekaru. Sojoji sun bayyana a gidan talabijan na Mali, inda suka yi jawabi kai tsaye ta bakin kakakin sojojin da suka yi juyin mulkin Kanal Ismaël Wagué: ''Mu sojojin da muka hadu a cikin wannan kwamiti na kishin kasa CNSP, mun kudiri aniyar daukar mataki a kan wannan al'amari a gaban al'umma da kuma tarihin da zai iya biyo baya domin ganin gwamnati ta ci gaba da yin aiki domin amfanin al'umma.''

Mali Kati PK Putsch Anführer Ismael Wague
Jagoran mulkin sojan Mali Ismael Wague a taron manema labaraiHoto: Getty Images/AFP/A. Risemberg

Sojojin sun yi kira ga kungiyoyin farar hula da 'yan siyasa da su bi sahunsu, sai dai har kawo yanzu babu wani martanin daga kungiyoyin farar hula na M5 wanda suka kwashe sama da watannin biyu suna yin bore a karkashin jagorancin Imam Dicko wadanda suka yi watsi da tayin sulhu da ECOWAS ta yi musu na warware rikicin siyasar cikin sulhu. An dai samu rahotanni fasawa tare da lalata gine-gine mallakar gwamnati, inda tuni mukaddashin hafsan sojojin saman kasar Malin Ismael Waguè wanda kuma ke zama kakakin sabon kwamitin ceto al'umar kasa wato National Commitee for the Salvationn of the Poeple ya yi kira ga 'yan kasar da su daina tashe-tashen hankulan da lalata gine-ginen gwamnatin.

A shekara ta 2013 ne aka zabi IBK a matsayin shugaban kasar Mali kafin ya sake samun nasara a shekara ta 2018 a zaben shugaban kasar, inda ya yi nasara a kan dan takarar adawa Soumaila Cisse wanda yanzu haka 'yan ta'adda ke yin garkwa da shi. Tuni dai kasashen Amirka da Faransa suka nuna kin amincewa da juyin mulkin na Mali wanda a nan gaba za a san yadda sojojin da suka yi juyin mulkin za su kwashe da kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO.