Taron kungiyoyin yan jarida a birnin Banjul na Gambia | Labarai | DW | 14.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kungiyoyin yan jarida a birnin Banjul na Gambia

Kungiyar yan jarida ta dunia Medecins Sans Frontieres, ta bayana shiga wata gagaranar kampe, ta neman yancin yan jarida a kasashen dunia.

Kungiyar, ta yi wannan bayani, albarkacin cikon shekaru 7, da mutuwar Norbert Zango, wani fittacen dan jarida, da ka hallaka a kasar Burkina Faso, a yayin da ya ke bincike, a kan kissan gillar da a ke zargin kanen shugaban kasa, Blaise Kampaore da aikatawa.

Da kuma alabarkacin cikwan shekara daya, da kissan gillar da a ka yi wa wani dan jarida, Deyda Diara, na kasar Gambia, a birnin Banjul, tsakanin daren 16, zuwa 17 ga watan Desember na shekara bara.

Bincike da hukumomin kasashe 2 ,su ka buda, don gano gaskiyar wannnan kashe kashe, har yanzu shuru kake ji ,wai kamar an shubka dussa, inji hausawa.

Gobe idan Allah ya kai mu, a birnin na Banjul, za a buda wani taro, da zai Magana a kan yanci yan jarida.

Sannanun yan jarida ,daga kasashe daban daban na Afrika, da turai,a tsawan kwanaki 2, za su masanyar ra´ayoyi, a game da batutuwan da su ka shafi, aikin jarida, a cikin tsari mulkin demokradiya.

Kungiyar Reportres sans Frontieres, na bukatar fadakar da dunia, a game da mahimancin aikin jarida, da kuma neman gurfanar da wanda a ka samu da hannu ,a cikin aikata ta´adancin kissan dan jarida.