Taron kungiyar SADC a Zimbabuwe | Siyasa | DW | 29.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron kungiyar SADC a Zimbabuwe

Ta yiwu batun kyamar baki a kasar Afirka ta Kudu ya mamaye taron kungiyar ci-gaban kasashen kudancin Afirka (SADC) da ake yi a Harare babban birnin kasar Zimbabuwe.

Shugaba Robert Mugabe na Zimbabuwe

Shugaba Robert Mugabe na Zimbabuwe

Shugaban kasar Zimbabuwe Robert Mogabe wanda kuma shine shugaban kungiyar ta SADC ya ce ya kadu matuka da abunda ya faru a Afirka ta Kudu. Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma dai na daga cikin shugabannin kasashen kungiyar ta SADC da ke halartar wannan taro. Ko da yake Mugabi ya nuna damuwarsa dangane da yadda 'yan kasar Afirka ta Kudu suka rinka kashewa tare da kona baki da ransu a biranen Johannesburg da kuma Durban a wani sabon salo na nuna kyamar baki a kasar, da ya zo jawabinsa na bude taron na SADC Mugabe ya kaucewa tabo abunda ya shafi kisan bakin a Afirka ta Kudu, inda ya bukaci kasashe 14 da ke cikin kungiyar ta SADC da su tabbatar sun inganta fitar da kayayyakin da aka riga aka sarrafa maimakon fitar da wadanda ba a sarrafa ba zuwa kasashen Asiya da Amirka da Kuma Turai tare da siyo wadanda aka sarrafa daga wadannan kasashen yana mai cewa.

Hanyoyin bunkasa tattalin arziki

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma

"Idan muka ci gaba da fitar da kayan da bamu riga mun sarrafa su ba dole za mu ci gaba da kasancewa cikin tarkon rashin ci-gaba, kana wadanda ke cin moriyar tattalin arzikinmu ba za su fasa ba. Ba wani ci-gaba da aka samu a yanayin ciniki tsakanin kasashen SADC. Mayar da hankali kan rage kudaden haraji da muka yi bai kawo ci-gaba a fannin tattalin arzikinmu da kuma rayuwar al'ummarmu ba."

Mugabe ya kara da cewa dolene su samarwa kansu mafita domin kwatar kansu daga Turawa 'yan mulkin mallaka da har yanzu suka gaza sakarwa kasashen Afirka mara su yi fitsari. Sai dai duk da wannan batu da Mugabe ke yi na ganin an inganta rayuwar al'ummar yankin kudancin Afirkan, kungiyoyin fararen hula da kuma manyan jam'iyyun adawar kasar sun yi watsi da taron suna masu cewa taron na birnin Harare ba zai yi wani tasirin azo a gani ba. James Maridadi na daya daga cikin 'yan majalisar wakilan kasar ta Zimbabuwe na jam'iyyar adawar ya ce kamata yayi 'yan jarida ma su kauracewa wannan taro inda yace.

Kyama da kisan baki a Afirka ta Kudu

Kyama da kisan baki a Afirka ta Kudu

Rashin 'yanci ga kafafen yada labarai

"Kamata ya yi 'yan jaridar Zimbabuwe su tunkari shugabannin kungiyar SADC su bayyana musu cewa shugabanku shine shugaban kasarmu, ya kirkiro dokokin da suke take hakkin kafafen yada labarai, saboda haka ku taimaka mana ku tilasta masa ya gyara wadannan dokoki ko ma yi aikinmu cikin 'yanci. Har yanzu muna da dokokin manyan laifuka na 'yan jaridu kuma suna daya daga cikin wadanda aka yi amfani da su tun lokacin yakin duniya na biyu. Ci gaba da amfani da wadannan dokoki na nuni da cewa dokokin kasarmu tsohon yayi ne."

Taken taron kungiyar ta SADC dai shine 'ci-gaban masana'antu' wanda akewa kallon zai iya tado da batun dalilin da ya sanya 'yan kasashen Afirka ke yin tururuwa zuwa Afirka ta Kudu domin neman abin dogaro da kai kasancewar ita ce kasar da tattalin arzikinta ya fi bunkasa a cikin kasashen kungiyar SADC din, duk kuwa da yadda 'yan kasar ke nuna kyama ga baki tare da yi musu kisan gilla.

Sauti da bidiyo akan labarin