Taron kolin kasashen G20 a Johannesburg
November 21, 2025
Yayin da birnin Johannesburg ke shirin karbar bakuncin taron G20 na Afirka na farko, Afirka ta Kudu na kokarin ta nuna tasirin da take da shi a fannin diplomasiyya da ma karfin tattalin arziki duk da kin halartar taron da Amurka ta yi. Tsawon makonni ke nan birnin Johannesburg da ke zama mafi girma a Afirka ta Kudu, ana gudanar da shirye-shiryen karbar bakuncin taron kasashen 20 masu karfin tattalin arziki na duniya G20
Dangantaka ta yi tsami tsakanin Washington da Afirka ta Kudu, saboda wasu dalilai. Da farko dai Amurka ta rage tallafin da take bayarwa ta hanyar hukumar bayar da agaji ta USAID cikin watan Fabarairu, abin da ya shafi rayuwar 'yan Afirka ta Kudu da dama wadanda ke samun tallafi musamman na magunguna.
Haka nan kuma an karawa Pretoria harajin fito mai yawan gaske, inda gwamnatin Donald Trump ba tare da wata kwakkwarar shaida ba ta zargi Afirka ta Kudu da kisan kiyashi a kan 'yan kasar fararen fata da ba su da rinjaye, zargin da Pretoria ta musanta.
Baya ga wannan kuma, Washington ta soki Afirka ta Kudu, kan karar da ta shigar gaban Kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ICC da ke birnin The Hague na kasar Holland, tana zargin Isra'ila da aikata kisan kiyashi a yankin zirin Gaza na Falasdinu, a yakin da take gwabzawa da kungiyar Hamas.
Wannan tsamin dangantaka ya sanya Amurka kaurace wa taron na bana, sai dai a ganin kwararre kan rikicin siyasa a cibiyar Signal Risk da ke Afirka ta Kudu Menzi Ndhlovu, kaurace wa taron na G20 da Amurka ta yi na da wata manufa ta daban. A cewarsa kokari ne na nuna cewa karar Afirka ta Kudu da shugabanninta, bai kai tsaiko ba a batun kasashen da ke fada a ji a duniya musamman a fannin tattalin arziki. Ya kuma shaidawa DW cewa:
"A zahiri matakin kaurace wa taron G20 da Amurka ta dauka, zai haifar da kalubale kasancewar Amurka ce ke iko ko kuma tana da fada a ji a fannoni da dama na gudanarwa a kungiyar G20. Dole sai mun yi taka-tsan-tsan, ga misali amsar da Afirka ta Kudu ta bai wa Trump ta dace. Ba ta nuna fushinta ba, sai ma ta mika goron gayyata ga dukka wanda zai halarta, wannan ne matakin farko. Mataki na biyu shi ne mai muhimmanci, yadda za ta samar da kudurori da za a iya aiki da su ba tare da Amurka ba, amma da amincewar kowa."
Ba ya ga batun matakin kaurace wa taron da Amurka ta dauka dai, matakin gwamnatin Afirka ta Kudu na nuna rashin tsoro ka iya zama babban kalubalenta. A hirarta da DW, shugabar Cibiyar Kawo Gyara ga Tattalin Arzikin Nahiyar Afirka wato African Center for Economic Transformation ACET a takaice Mavis Owusu-Gyamfi ta bayyana cewa, a yankin Kudu da Saharar Afirka akwai ka'idoji da kuma al'ada ta hada kai yayin rikici ko matsala. A cewarta tana alfahari da yadda Afirkan ta dauki wannan mataki, inda ta kara da cewa:
"Ina tunanin taron ya zo a daidai lokacin da duniya ta fara gane cewa, Afirka ce cibiyar magance matsaloli da dama da duniya ke fuskanta. Na farko tattalin arzikin nahiyar na bunkasa cikin hanzari, kana tafi kowacce nahiya yawan matasa masu tasowa. Kamar yadda kowa ya sani, nan da shekara ta 2030 Afirka za ta kasance nahiyar da za ta wakilci kaso daya bisa uku na ayyukan yi a duniyar da ke kara tsufa cikin sauri. Tana da albarkatun kasa masu yawa da ake bukata domin samar da tsaftataccen yanayi, a daidai lokacin da duniya ke fuskantar sauyi ko dumamar yanayi. A dangane da haka, ci-gaban duniya da samun daidaito a cikinta ya ta'allaka ne a kan hanyar da Afirka ta dauka mai bullewa ce ko akasin haka."
Gwamnatin Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu dai, na fama da tarin matsaloli da suka hada da cin-hanci da yawan aikata laifuka da tsayawar tattalin arziki da kuma matsalar rashin aikin yi.