1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta tattauna kan rigakafin corona

February 25, 2021

Shugabanin Kungiyar Tarayyar Turai za su tattauna yadda za a gaggauta samar da karin rigakafin annobar coronavirus a turai da matsaya kan takardar shaidar rigakafin.

https://p.dw.com/p/3pq0z
Brüssel Videokonferenz | Ursula von der Leyen, EU-Kommissionspräsidentin
Hoto: picture-alliance/AP Photo/F. Seco

Taron da zai gudana ta kafar internet da shugabanin kasashe 27 na kungiyar na zuwa ne shekara guda bayan bullar annobar coronavirus, yayin da yawancin kasashen turai ke fuskantar annobar karo na biyu ko na uku.

Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce duk da takaddamar da ta auku da kamfanin AstraZeneca, kamfanonin samar da rigakafin abokan huldarsu ne a lokacin wannan annobar.

Jami'an kungiyar da kuma na diflomasiyya sun yi gargadin cewa ya zuwa yanzu ya yi wuri a fara amfani da takadar shaidar rigakafin annobar coronavirus don saukaka tafiye-tafiye.