1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Taro kan rikicin Gaza

November 11, 2023

Shugabannin kasashen Larabawa da Musulmai sun fara taron ganawa a birni Riyadh na kasar Saudiyya domin jaddada mahinmancin kawo karshen luguden wutar da Isra'ila ke ci gaba da yi wa yankin Zirin Gaza na Falasdinu.

https://p.dw.com/p/4YhJD
Saudiyya | Taron kasashen Musulmai a birnin Riyadh
Taron kasashen Musulmai a kasar SaudiyyaHoto: WANA NEWS AGENCY/REUTERS

Ana gudanar da taron gaggawan ne makonni biyar bayan barkewar rikici tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas, wanda kawo yanzu ya yi ajalin mutane 1,200 a bangaren Isra'ila yayin da Falasdinawa 11,000 suka halaka ciki har da kananan yara kimanin 4,500.

Karin Bayani: Blinken ya kammala ziyara a Gabas ta Tsakiya da Asiya

Saudiyya | Taron kasashen Musulmai a birnin Riyadh
Taron kasashen Musulmai a kasar SaudiyyaHoto: WANA NEWS AGENCY/REUTERS

Gabanin buda taron kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya ya bayyana cewa kasashen na son cimma matsaya guda daya a game da hatsarin wannan tashin hankalin da ba a taba ganin makamancinsa ba a zirin Gaza da yankunan Palastinawa ba.

Daga cikin mahalarta taron har da shugaban kasar Iran Ebrahim Raissi, kuma wannan ne ma ke zama karon farko da wani shugaban Iran din ke ziyarartar Saudiyya tun bayan kawo karshen zaman doya da man ja na shekaru bakwai tare da dawo da huldar diflomasiyya tsakanin manyan kasashen biyu na Gabas ta Tsakiya.

Dama dai a jajibirin buda taron Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohamed ben Salman a jawabinsa na farko a bainar jama'a kan rikicin na Gaza, ya yi Allah wadai da cin zarafin fararen hula da kuma keta dokokin kare hakkin bil adama na kasa da kasa da sojojin mamaya na Isra'ila ke yi a dan karamin yankin na Falasdinu.