Taron Africa Business Week 2013
March 26, 2013Talla
A ranakun 22 zuwa 26 ga watan Afrilu ake gudanar da taron mako na Africa Business Week a birnin Frankfurt. Taron na tsawon mako guda zai duba batutuwan da suka shafi ciniki da haɗin kan tattalin arziki tsakanin ƙasashe Afirka da na Turai. Tashar Deutsche Welle dake zama abokiyar haɗin guiwa ta fannin yaɗa labarai a taron na Afrika Business Week, ta gabatar da jerin rahotanni na binciken da wakilanta suka yi game da noma da kiwo a kasashen Afirka.