190413 Afrika Pflanzenschutzmittel
April 25, 2013Duk da cewar magungunan kashe kwari da kuma tsirran da ke hana samun anfani gona mai yawa na da mummunar illa ta fuskar gurbata muhalli, amma kuma yana da alfanun gaske wajen bunkasa anfanin gona. Sai dai kuma ba safai ake anfani da irin wannan sinadari a nahiyayr Afirka ba, wanda rashin anfani da shi kuma ke haddasa lalacewar dimbin hatsin da kimarsa zai iya kaiwa na kudi miliyoyin Euro a nahiyar ta Afirka:
Wannan dai wata na'urar inganta irin masara ce ta hanyar sanya mata magungunan kashe kwari da kuma na kaucewa ilar tsirrai bayan shuka ta, sakamakon zuba mata wasu sinadaran kimiyya mai kama da hoda.
Sinadaran kimiyyar, wanda aka yi ta gwaje-gwajensa a dakunan binciken kimiyya da ke nan Jamus, wani kanfanin kasar mai suna BASF Schlotterbeck da ke nan Jamus ne ke samar da shi, kuma a cewar jami'in kanfanin Dakta Ulf Schlotterbeck, burin daya ke son cimma shi ne bada kariyar da ta dace ga masara, kana manoma su sami albarkatun noma masu yawa a nahiyar Afirka bisa la'akari da illar da irin wannan nau'i da tsirrai ke yawaita yiwa masara a nahiyar :
Ya ce " Ga manoman da ke zaune a yankunan da ke fama da matsalar tsirran da ke hana samun anfani gona sosai, sinadaran da kanfaninmu na BASF da ke Jamus ke samarwa zai ba su damar samun anfani mai yawa a dan karamin filin da suke da shi, saboda zai yi matukar rage kaifin matsalolin karancin anfani da suke fama da shi."
Matsalar tsirran dake hana girbe masara mai yawa dai, ta fi zama ruwan dare gama duniya ne a yankin gabashin Afirka, inda kuma kanfanin da ke sarrafa sinadaran yaki da shi, ya kulla kawance tare da gidauniyar "Bill da Melinda" kuma suka samar da irin masarar da aka sanyawa wannan sinadarin kimiyyar da zai tabbatar da cin gajiyar da ta dace daga noman masarar, wanda kuma tuni manoma a kasar Kenya suka fara cin anfanin gwajinsa.
Sammy Waruigi, babban jami'in kanfanin BASF da ke samar da irin masarar da aka sanyawa sinadaran kimiyyar, ya ce tuni kananan manoma a kasar suka fara ganin alfanun gwajin da suka yi a wasu filayen nomansu:
Ya ce " Manoman da suka yi gwajin wannan nau'i na irin masara a rubu'in filayen nomansu, na bayar da tabbacin cewar suna cin gajiyar da ta ribanya - har sau ukku idan an kwatanta da irin albarkar da suke samu a sauran tsulutsin filayen noman. Wannan tabbaci ne ga manomin na cewar makomar nomansu ta dogara ne ga cin gajiyar da ke tattare da wannan nau'i na irin masara mai sinadarin kimiyya."
A bisa wannan dalilin ne a cewar jami'in, manoma a kasar ta Kenya ke yin tururuwa wajen yin anfani da sabon iri na masarar:
Ya ce " Wannan sabuwar fasaha na ci gaba da yaduwa cikin gaggawa. Muna ta shirya tarukan ilimantarwa, inda muke nunawa kananan manoma hanyoyin fahimtar fasahar."
Kanfanin BASF da ke samar da irin masarar ya tashi tsaye, ba wai kawai ga kokarin samar da irin masarar da ke kaucewa illar kwari da kuma tsirran da ke lalata anfani ba, a'a harma da gwaje-gwajen kimiyyar da za su sanya kanfanin zuwa filayen noma a nahiyar Afirka da kuma taimakawa manoman nahiyar bunkasa kudaden shigarsu daga sana'ar.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman