Sharhi: Ko Afirka za ta iya dakile matsalar yunwa? | Zamantakewa | DW | 26.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Sharhi: Ko Afirka za ta iya dakile matsalar yunwa?

Duk da cewa nahiyar Afirka ka iya magance matsalar yunwa, amma tana rashin kyakkyawar niya a siyasance inji Ludger Schadomsky a cikin wannan sharhi.

Wani labari mai kyau dangane da gwamnatocin Afirka, shi ne a yanzu kasashen dake bada taimakon raya kasa da Majalisar Dinkin Duniya, sun sake gano muhimmancin bangaren kula da harkokin noma a nahiyar Afirka. Kusan shekaru ishirin da suka gabata dai sun mayar da hankali kan bangaren masana'antu. Inda fannin noma bai samu wata kulawa ba.

Da farko dai 'yan siyasa farka ne da ganin halin kayayyakin masarufi suke a kasuwannin, daura da matsaloli na karancin abinci da matsanancin yunwa da aka fuskanta a shekara ta 2008. A dangane da hanyoyin neman mafita daga wannan matsala ne, a yanzu haka ma'aikatar kula da taimakon raya kasashen ketare ta nan tarayyar Jamus ta ke kaddamar da sabbin matakai dake mayar da hanakali kan farfado da bangaren noma. A nahiyar Afirka dai akwai kimanin mutane miliyan 900, kuma kashi 90 daga cikin 100 na yawan al'ummarta suna dogaro ne da harkokin noma. Ana iya misalta hakan da wani batu makancinsa; misali waye a nan tarayyar jamus zai bada shawarar cewar, ayi watsi da kanana da matsakaitan sana'oin hannu, dake kasancewa tabbabacen miliyoyin wuraren aiki domin karkatar da tattalin arzikinta?

Menene muhimmancin bangaren noma a Afirka?

Harkar noma dai na nufin rayuwar bil Adama. Ko wane mutum daya cikin takwas a fadin duniya nan ba shi da isasshen abincin da zai ci. Mafi yawan mutanen dake fama da matsananciyar yunwa da karancin abinci dai suna zaune ne a yankin kudancin Asia da yankin kudu da sahara a nahiyar Afirka. Wannan dai batu ne na razanarwa. A kan haka ne tashar DW ta tsara shiri na musamman na gudanar da bincike da samar da mafita dangane da wannan matsalar mai taken, "shin za'a iya dakatar da matsalar yunwa a Afirka kuwa?" Shin Afirka za ta iya samar da abincin da zai wadata al'ummarta a wannan duniya dake kara bunkasa? Ko kuma, shin nahiyar za ta iya samar da isasshen abincin da za ta iya magance matsalar yunwarta watakila har ma ta fitar da abinci zuwa ketare?

Binciken dai ya mayar da hankali ne kan yankunan gabashi da yammacin Afirka, da kuma dakunan binciken kimiyya dake nan tarayyar Jamus, sakamakon da ke amsa dukkan tambayoyin dake sama: ko shakka babu za a warware matsalar yunwa da karancin abinci idan har za a samu hadin kai tsakanin 'yan siyasar nahiyar da kasashen dake bada taimakon raya kasa.

Babu sukunin zuba jari

Sai dai akwai bayan wannan labarin ba mai dadin ji ba ne. Kasancewar a kasashen Afirka masu yawa, har yanzu manoma na fuskantar karancin sukunin da zasu zuba a gonakinsu, domin samun bunkasar abinci da zasu iya ciyar da akansu balle tana was. Alal misali shine kasar Ethiopia, ina kashi 85 daga cikin al'ummar kasar kusan miliyan 90, suna rayuwa ne a kan albarkatun noma. Amma gwamnatin kama karya ta kasar ta haramta mallakan filaye. Ko filayen da ake bada hayarsu ga jama'a ma babu tabbaci a kansu. Manoman basu da issasun kudaden da za su kashe wajen kare matsalar zaizayar kasa dake addabar 'yan kananan filaye da gwamnati kan ara musu. A maimakon haka suna ajiyar iri mai tsada da akan hada shi da sinadaran dake lalata shi, wanda daga karshe za su yi asarar girbi, kana basussuka za su karu.

Har yanzu manoman Afirka basa samun rancen da suke bukata daga wajen bankuna. Wanda hakan ne zai taimaka wajen basu damar sayen manyan na'urorin aikin gona, domin maye gurbin kana da yanzu suke amfani dasu, kazalika zai bunkasa amfani. Har ya zuwa wannan karni na 21 da ake ciki dai manoman Afirka na fama da matsalolin rashin samun damar shigar da kayayyakin kasuwannin duniya. Hanyoyin zuwa kasuwanni mafi kusa ma ba abun azo a gani bane. Bincike ya nunar da cewar kashi 50 daga cikin 100 na danyan kayyakin amfanin gonar manoman afrika yana lalacewa ne kafin ya isa kasuwar da za'a sai dasu. Jerin matsalolin da 'yan kasuwar Afrika ke fuskanta dai basu da iya.

Bunkasa masana'antun Afirka ba ta yiwuwa sai tare da aikin noma

Binciken wakilin DW yana nunar da cewar, ba wani abun a zo a gani manoman Afirkan ke bukata na inganta ayyukansu ba. Ya zamanto wajibi a tursasa wa kamfanonin Afirka dangane da bukatar tallafa wa manoman Afirka. Alal misali kada a ce sai an kawo koko daga birnin Abidjan na kasar Cote d'ivoire zuwa birnin Hamburg domin sarrafawa.

Akwai damarmaki masu yawa ga wannan nahiya. Zanga zangar tsadar rayuwa da ta gudana a Tunisiya a shekara ta 2011, wanda ta tilasta 'yan siyasa ajiye mukamansu, da guguwar sauyi da ta kada daga yankin arewacin Afirka zuwa duniyar Larabawa, na masu zama gargadi na musamman ga shugabannin Afirka. Yunwa dai na mai zama wani babban makami ne da talakawa ke da shi na yakar 'yan siyasa. Dangane da haka ne za a iya cewar lokaci yayi da nahiyar Afirka za ta samar wa da harkokin noma sabuwar makoma.

Mawallafa: Ludger Schadomsky / Zainab Mohammed Abubakar
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin