Taron ƙasashen duniya a kan Siriya | Labarai | DW | 30.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ƙasashen duniya a kan Siriya

Wakilai a taron na Vienna, za su yi ƙoƙarin samar da hanyoyin kawo ƙarshen rikici Siriya.

Manyan ƙasashen duniya waɗanda suka haɗa da Amirka da Rasha da Birtaniya da Faransa da kuma Jamus.Za su tattauna makomar shugaba Bashar al Assad wanda bisa ga dukkan alamu ake da saɓannin ra'ayoyi tsakanin ƙasashen da Rasha.Wacce ta dage kan msatsayin cewar al ummar ƙasa ita ce ke zaɓen shugaba, yayin da sauran ƙasashen ke neman a cire shugaba Bashar ɗin daga mulki da ƙarfin tuwo.

A karon farko za a yi gwa da gwa a taron tsakanin Iran mai goyon bayan Siriya da kuma Saudiyya wacce ke mara wa 'yan adawar baya.