Taro koli kan yaki da cutar Ebola | Siyasa | DW | 02.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taro koli kan yaki da cutar Ebola

Jami'an kiwon lafiya da wakilan gwamnatoci da kungiyoyin bada agaji sun gudanar da wani taro a Burtaniya domin yaki da cutar Ebola.

Taron dai ya hada kan masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya musamman ma dai cutukan da ke saurin yaduwa irinsu Ebola. Yayin gudanar taron, William Pooley, wani ma'aikacin jinya dan asalin Burtaniya da ya kamu da cutar Ebola ya ce irin kuncin da masu dauke da ita kan shiga abun razanarwa ne matuka.

William Pooley während einer Presskonferenz

William Pooley da ya warke daga cutar Ebola ya ce masu fama da ita na cikin kunci

Tun lokacin da aka gano wannan cuta ta Ebola kusan shekaru Arba'in da suka gabata, wasu na ganin kasashe masu karfin tattalin arziki da ke kirkiro magunguna sunyi ko burus da ita ne ganin cewa a nahiyar Afrika ne kadai ake kamuwa da ita, in banda kawo yanzu da ta bulla a Turai da Amurka to sai dai kasashen sun musanta haka.

Da ya ke tsokaci yayin taron, sakataren harkokin wajen Burtaniya Philip Hammond cewa ya yi "wannan cuta sai kara yaduwa ta ke babu kakkautawa a lokaci guda kuma kasashen duniya sai yi wa matsalar rikon sakainar kashi suke". Sakataren na harkokin wajen na Burtaniya ya kara da cewa a yanzu lokaci ya yi da dole za a farka a zage damtse domin yaki da wannan cuta ganin yadda ta ke kara yaduwa.

Gwamnatocin Burtaniya da Saliyo ne suka dauki nauyin shirya wannan taro, kuma a iya cewa shi ne taro na baya-bayan a irin wadanda ake gudanarwa da nufin ganin an yi musayar yawu dangane da yunkurin da ake yi na ganin an kawar da cutar Ebola baki daya, to sai dai wannan mafarki da ake da shi na kara dakushewa duba da yadda kayan aiki da magunguna da karancin ma'aikata ke sanya cutar na kara bazuwa musamman ma kasashe irin su Liberiya da Saliyo.

Sierra Leone Ebola September 2014

Hukumomi sun ce yaki da cutar Ebola na da wahalar gaske

Wani abu har wa yau da ke yin kafar ungulu ga wannan yunkuri shi ne irin yadda mutane ke bijirewa zuwa asibitoci don neman magani in sun kamu da cutar da ma rashin cikakken ilimi na yadda ake kamuwa da cutar da yadda ta ke yaduwa tsakankanin mutane musamman ma dai a yankunan da ke da cinkoso.

Sauti da bidiyo akan labarin