Tarihin tutar da ake gani a bayan kujerar shugaban Najeriya | Amsoshin takardunku | DW | 26.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin tutar da ake gani a bayan kujerar shugaban Najeriya

Wata tuta da ake gani a bayan shugaban Najeriya baya ga tutar kasa, ita ce tutar sojoji wadda take nuna cewa shugaban ke zama babban kwamandan askarawan kasar

Tutar Najeriya da kuma wata tutar da ake gani a bayan kujerar shugagba ta sojoji ce, wadda ta kunshi tutar sojin kasa, da na ruwa da kuma na sama. Ita wannan tuta take nuni da cewa shugaban kasa shi ne kuma babban komandan hafsoshin mayakan Najeriya.

Duk kasdashe duniya suna amfani da irin wannan tuta wa shugaban gwamnati, abin da ke nuni da karfi da kasa take dogara a kai. Daya daga cikin aikin sojoji shi ne tabbatar da tsarin kasa da kare kasa daga barazana.