Tarihin tsohon shugaban Saliyo | Amsoshin takardunku | DW | 07.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin tsohon shugaban Saliyo

Tarihin tsohon Shugaban kasar Saliyo Marigayi Ahmad Tejan Kabbah

An haifi Marigayi Ahmad Tejan Kabbah ranar 16 ga watan Febrairun shekarar 1932 a kauyen Pendembu, na Gundumar Kailahun yanakian gabashin kasar Saliyo, iyayensa Musulmai wadanda ke da alaka da sarauta.

Marigayi ya girma a Freetown babban birnin kasar inda ya halarci makarantun Primary da Secondary, kafin daga bisani ya zarce kasar Birtaniya da ya samu digiri a fanfanin tattalin arziki a Jami'ar Wales. Sannan ya koma kasar Saliyo ya fara aiki da gundumar yammacin kasar har zuwa mukamin Kwamishinan Lardi, kana ya zama babbar sakatare.

Marigayi Alhaji Ahmad Tejan Kabbah ya koma aiki da Majalisar Dinkin Duniya, inda ya shafe kusan shekaru 20 yana aiki da hukumar kula da ayyukan ci-gaba na majalisar. Ya zauna a kasashen Tanzaniya da Uganda, da kuma Zimbabwe kafin ta samu 'yanci. Kafin ya yi murabus a shekarar 1992 Kabbah ya shiga cikin masu manyan mukamai a helkwatar hukumar kula da ci-ciga da Majalisar Dinkin Duniya, UNDP, da ke birnin New York na kasar Amirka.

Ahmad Tejan Kabbah ya koma gida bayan ya yi murabus, inda bayan juyin mulki na shekarar 1992 aka umurce shi da ya jagoarnci wata hukumar ba da shawara kan yadda za a mika mulki wa farar hula da rubuta sabon kundin tsarin mulki. Kuma daga bisani na kusa da Kabbah sun nemi ya tsaya takara yayin zaben shekarar 1996, zaben da ya lashe yayin da jam'iyyarsa ta SLPP ta samu galibin kujerun majalisar dokoki.

Tejan Kabbah ya dauki madafun iko lokacin da yakin basasan kasar Saliyo ke gauniya, abin da ya janyo sojoji suka yi yunkurin kifar da gwamnatin karkashin Major Johnny Paul Koroma a shekarar ta 1996. Duk da rashin nasara bayan shekara guda ranar 25 ga watan Mayun shekarar 1997 sojoji sun kifar da gwamnati tare da fito da Major Johnny Paul Koroma wanda aka nada shugaban gwamnatin mulkin soja. Amma sojojin Afirka ta Yamma karkashin Najeriya sun tsere da Shugaba Tejan Kabbah zuwa kasar Guinea Conakry. Daga bisani sojojin na Najeriya sun fatattakin sojojin da suka yi juyin mulki inda a ranar 8 ga watan Febrairun shekarar 1998 Shugaban gwamnatin mulkin sojin Najeriya Marigayi Janar Sani Abacha ya jagoranci mayar da Ahmad Tejan Kabbah kan karagar mulkin Saliyo.

Duk yunkurin da Shugaba Kabbah ya yi na sasantawa da 'yan tawaye na kungiyar RUF ya ci tura, domin suna kunce yarjejeniyar tare da ci gaba da fada da zaran an dawo daga wajen saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya. Rikici ya ci gaba inda a farkon shekarar 1999 Firamnistan Birtaniya na lokacin Tony Blair ya tura da dakaru domin dakile hanzarin 'yan tawaye da karfafa aikin sauran dakarun kiyaye zaman lafiya. Wannan hadin gwiwa na Birtaniya da sauran sojojin kasashen Afirka ta karya lagon 'yan tawaye wadanda suka amince da kunce damara a shekarar 1999 tare da tura dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya. Tejan Kabbah ya bayyana kawo karshen yakin basasan kasar ta Saliyo a shekara ta 2002.

A wannan shekara da gagarumin rinjaye Ahmad Tejan Kabbah ya sake lashe zabe karo na biyu kuma na karshe, inda ya sake mulkin shekaru biyar zuwa shekara ta 2007. Bayan zaben shekara ta 2007 da madugun 'yan adawa Ernest Bai Koroma ya lashe, Kabbah ya yi murabus daga harkokin siyasa.

Marigayi Ahmad Tejan Kabbah ya haifi yara biyar da matarsa ta farko Patricia Kabbah, malamar makaranta, wadda Kirista ce, ta bar duniya lokacin yana shugaban kasa a shekarar 1998. Ya sake aure a shekara ta 2008 tare da Isata Jabbie Kabbah. Marigayin ya bar duniya ranar 13 ga watan jiya na yana da shekaru 82 da haihuwa.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu