Tarayyar Turai ta goyi bayan Macron
April 24, 2017Talla
Tarayyar Turan dai ta ce goyon bayanta ga Macron da dalili, kasancewarsa mai ra'ayin kare kimar Turawa ne sama da wadda ta ce aniyar ta ba abar amincewa ba ce.
Dan takara mai zaman kansa Emmanuel Macron mai shekaru 39, ya yi nasara a zagayen farko, za kuma su kara da malama Le Pen a ranar 7 ga watan gobe na Mayu.
Macron dai tsohon ma'aikacin banki ne da kuma ya rike ministan tattalin arziki a gwamnati mai ci kafin daga bisani ya yi murabus ya kafa sabuwar jam'iyyarsa.
Idan har ya kaiga lashe zaben kasar, Mista Macron zai zama shugaba na farko ma fi karancin shekaru a tarihin kasar Faransa.