1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tankar mai ta fashe da mutane a Saliyo

Abdul-raheem Hassan
November 6, 2021

Rahotanni na cewa tankar mai ta fashe ne sakamakon hatsari da wata motar safa a wani gari da ke gabashin Freetown babban birnin kasar Saliyo da yammacin ranar Juma'a.

https://p.dw.com/p/42fR3
Sierra Leone Tanker Explosion Freetown
Hoto: SAIDU BAH/AFP/Getty Images

Shedu sun ce tankar ta tarwatse da mutane da dama yayin da gobara ta tashi da dandazon jama'a ke diban man fetur da ke tsiyayewa bayan faduwar tankar, hukumomi sun ce wadandan suka kone na cikin mawuyacin hali a gadon jinya.

Wasu hotunan bidiyo a shafukan sada zumunta bayan hatsarin ya nuna mutanen da gobara ta kama kayansu suna konewa a cikin yanayi na tausayi, Shugaban kasar Julius Maada Bio, wanda ke birnin Glasgow na yankin Scotland yana halartar taro kan sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana alhininsa kan asarar rayukan da aka yi a hatsarin, yayin da mataimakinsa Mohamed Juldeh Jalloh ya ziyarci asibitoci biyu da ake jinyar wadanda suka kone, ya kuma yi alkawari aiki da hukumomin agaji don kai dauki.