1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Shirin sayar da abinci da rangwame

July 24, 2023

Bayan share tsawo na lokaci cikin halin rudu, gwamnatin tarrayar Najeriya ta ce tana shirin fara raba abinci da raguwar kaya na tallafin rage radadin zare tallafin man fetur.

https://p.dw.com/p/4UKAp
Nigeria Reis-Pyramide gegen den Hungersnot im Land
Hoto: Ubale Musa/DW

kama daga babban bankin CBN ya  zuwa ga rumbunan ajiyar na gwamnatin kasar 33  dai 'yan mulkin Najeriyar sun ce suna da akalla buhu miliyan 50 da nufin rage radadin da ke neman zauta 'yan kasar a halin yanzu. Jihohin kasar 36 ne dai za su jagoranci shirin da a karkashin sa za'a sayar da abinci da sauki ga masu bukata a fadar Inuwa Yahaya da ke zaman gwamnan Gombe kuma shugaba na kungiyar gwamnonin arewacin kasar in da barazanar ta abinci ke zaman mai girma ya ce shirin zai taimaka. Duk da cewar babban bankin kasar na CBN ya ce ya yi nisa cikin shirin tare da sauyin buhuna da nufin kaucewa wasoso cikin kasar da ke karatun ni yasu, akasin alkawarin 'yan mulkin babu alamun fara rabon a mafi yawa na wurare. Kabir Ibrahim dai na zaman shugaban kungiyar  manoman tarrayar Najeriyar ta AFAN da kuma ya ce babu alamun fara shirin a ko'ina cikin kasar a halin yanzu.

Ko gwamnatin Najeriyar za ta cika alkawarin da ta dauka zuwa ga al'umma

Bola Ahmed Tinubu shugaban kasar Najeriya
Bola Ahmed Tinubu shugaban kasar NajeriyaHoto: Sunday Aghaeze/AP Photo/picture alliance

Babban rikicin dai ya zuwa yanzu na zaman iya kai wa ya zuwa cika alkawarin taimaka wa mutane miliyan 50 da ke da bukata ta talalfi cikin kasar a halin yanzu. Majioyyi dai sun ce ko bayan tan dari biyu ko kuma buhu miliyan daya da babban bankin CBN ke takama da shi. Mohammed Magaji da ke sana'ar noman, abincin da ke a rumbuna na gwamnatin bai taka kara ba balle kai wa ya zuwa ga bukatar miliyoyin na 'yan kasar da ke bukatar sauki. Akalla tan dubu 72 ne dai ake zargin daka wasoso a karkashi na tsohuwa ta gwamnatin in da mafi yawan hatsin ya koma makami na siyasa  cikin kasar.