1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban ta tsagaita wuta a Afghanistan

May 24, 2020

Shugaba Ashraf Ghani na kasar Afghanistan, ya yi marhabin da sanarwar tsagaita buda wuta da mayakan Taliban suka yi, yayin da duniya ke lokaci na Sallah karama.

https://p.dw.com/p/3chh9
Afghanistan Kabul | Taliban werden aus dem Bagram Gefängnis entlassen
Hoto: Reuters/National Security Council of Afg

Kungiyar Taliban, ta sanar da tsagaita wutar ce ta kwanaki uku, bayan kammala Azumin watan Ramadan.

Shugaba Ghani na Afghanistan din ya ce ya tsawaita wa'adin shirin maida wuka kube tsakanin gwamnati da kungiyar.

Hakan kuwa ya zo ne kwanaki kalilan bayan wakilin Amirka a shirin samar da zaman lafiya  aAfghanistan din Zalmay Khalilzad, ya kai ziyara biranen Kabul da ma Doha na kasar Katar.

Wakilin na Amirka ya bukaci bangarorin na Taliban da gwmanatin Afghanistan su rage kai wa juna hare-hare.

A jawabin da ya gabatar wa mayakan Taliban, jagoran kungiyar ya bayyana aniyarsu ta cimma zaman lafiya da bangaren gwamnatin na Afghanistan.