1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran za ta hana IAEA sa ido kan nukiliyarta

Abdul-raheem Hassan
February 15, 2021

Gwamnatin Tehran ta yi barazanar taka wa hukumar lura da makaman nukiliyar duniya wato IAEA sa ido kan ayyukan sarrafa makamanta, in ba a warware takaddamar da ke tsakaninta da Amirka a karshen wannan wata ba.

https://p.dw.com/p/3pNjE
Iran Urananreicherungsanlage Isfahan
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Taherkenareh

Ma'aikatar harkokin wajen Tehran ta ce muddin ba a cimma kaddamar da yarjejeniyar nukiliya bisa tsari ba a karshen wannan wata, to tabbas Iran na da ikon yin watsi da ka'idojin hukumar IAEA. 

Takaita sa ido kan cibiyoyin nukiliyar Iran na cikin yarjejeniyar da kasashen duniya suka cimma a 2015 a birnin Vienna, matakin da ya takawa Iran din birki daga gina tasohin nukiliya a matsayin makami. Sai dai janyewar Amirka daga yajejeniyar a mulkin Donald Trump, ya fusata Iran fara karya ka'idojin.