Takaddama tsakanin Rasha da Birtaniya | Labarai | DW | 08.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takaddama tsakanin Rasha da Birtaniya

'Yan sanda a Birtaniya na kokarin tantance wanda ya yi amfani da guba mai tsananin hadari a wani yunkuri na yin kisa a kan tsohon jami'in leken asiri na Rasha da yar'sa a kudancin Birtaniya.

Bildkombo - Sergei Skripal und seine Tochter Yulia

Serguei Skripa tare da yar'sa Yulia

Serguei Skripal dan shekaru 66 da yar'sa Yulia mai shekaru 33, an taras da su a cikin wani yanayi na dogon suma  a ranar Lahadin da ta gaba a kudancin Birtaniya. Kanal Serguei Skripal tsohon jami'n leken asiri na Rashar wanda aka yanke wa hukuncin daurin shekaru 13 a shekara ta 2006 saboda samunsa da laifin sayar da bayyanan siri ga Birtaniya. A shekara ta 2010 a wata musayar ta fursunoni da aka yi tsakanin Birtaniya da Rasha, Birtaniya ta fansheshi ya dawo da zama a Birtaniya.