1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aljeriya: Adawa da takarar Bouteflika

Mahmud Yaya Azare RGB
March 4, 2019

Bayan mika takardun neman tsayawa takarar shugabancin kasar a karo na biyar, takaddama ta barke tsakanin masana doka kan sahihancin wannan takarar na Shugaba Abdelaziz Bouteflika da ya kwashi dogon lokaci yana jinya.

https://p.dw.com/p/3EPNN
Photo by RYAD KRAMDI / AFP)        (Photo credit should read RYAD KRAMDI/AFP/Getty Images) - Vor Benutzung Rechte klären!
Shugaba Abdelaziz Bouteflika, yana fama da cutar shanyewar bangaren jikiHoto: Getty Images/AFP/R. Kramdi

Shugaban na Aljeriya dan shekaru 81 da haihuwa, yana fama da cutar shanyewar jiki tun kusan shekaru shidan da suka gabata, wakilinsa kuma sabon shugaban yakin neman zabensa, Abdulgani Za'alan wanda a madadinsa ya gabatar da takaddunsa na neman tsayawa takara a ofishin hukumar zabe, ya karantawa 'yan kasar jawabin Shugaban da ke cewa..

 "Na dauki alkawari gaban Allah da  gabanku ya ku 'yan Aljeriya cewa, da zarar kun sake zaba na a karo na biyar, cikin tsukin shekara guda, zan shirya taron kasa da zai tsara sabon kundin tsarin mulki, kana zan gudanar da zaben gaggawa na shugaban kasa wanda ni bazan tsaya takara cikinsa ba. Na yi ammanar cewa, yin hakan, zai kai ga cimma muradunku na kawo sauyi a kasar nan cikin lumana.''

Algerien Algier - Proteste gegen Abdelaziz Bouteflika gegen weitere Amtszeit
Masu zanga-zanga sun yi fatali da tayin Shugaba Bouteflika na ci gaba da mulkiHoto: Imago/Xinhua

Tuni galibin 'yan takarar shugabancin kasar, wadanda a jiyan suka janye takarar tasu ,da shuwagabannin jam'iyyun adawa  suka yi kira ga 'yan kasar da su ci gaba da yin zanga-zanga, domin a cewarsu, ga dukkan alamu, akwatin zabe a kasar bai da wani amfani. Ga alama irin wannan kiran ya samu karbuwa, ganin tun a daren jiya Lahadi fadar mulkin kasar Aljaz ta yi cikar kwari da masu zanga zanga.

A jiya Lahadin ne, wa'adin mika takaddun takarar shugabancin kasar ke karewa, kuma kundin tsarin mulkin kasar ya fayyace cewa, dole ne dan takara ya mika takaddunsa da kansa ba ta hanyar wakilci ba, lamarin da ya sanya masharhanta ke nuna fargabar cewa, zai yi wuya, kan dai ba'a murde wuyan doka za ayi ba, hukumar zaben ta bai wa Bouteflika shedar cancantar tsayawa takara, bayan ta yi nazarin takaddunsa nan da kwanaki goma, kamar yadda dokar zaban kasar ta tsara.