Taiwan da Amirka na kara zumunta duk da gargadin China | Labarai | DW | 18.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taiwan da Amirka na kara zumunta duk da gargadin China

Sakatare janar na jam'iyyar DPP Joseph Wu ya tafi kasar Amirka a ranar Litinin din nan bayan da mahukuntan birnin Beijing ke ci gaba gargadin Taiwan ta manta da batun neman ballewa.

Jaushieh Joseph Wu

Sakataren jam'iyyar DPP Joseph Wu

Wani babban mamba daga jam'iyyar da ke fafutikar 'yancin Taiwan daga China zai ziyarci Amirka bayan da jam'iyyarsu ta DPP ta samu gagarumin rinjaye a zaben da ya gudana a karshen mako, wani lamari da ke nuna kullewar dangantaka tsakanin kawayen juna yayin da Amirkar ke zame wa Taiwan wurin samun makamai.

Ziyarar ta sakatare janar na jam'iyyar ta DPP Joseph Wu wacce ya tafi kasar ta Amirka a ranar Litinin din nan, na zuwa ne bayan da mahukuntan birnin Beijing ke ci gaba gargadin Taiwan ta manta da batun neman ballewa .

Jam'iyyar Tsai Ing-wen ta DPP dai ta samu gagarumin rinjaye a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa da ya gudana a karshen mako, wani abu da ya sake nuna shiga sabuwar tankiya da China wacce ke bayyana cewa koda da karfin tuwo ba za ta bari yankin na Taiwan ya kubuce mata ba.