Taimakon sassan jiki na roba ga nakasassu | Zamantakewa | DW | 13.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Taimakon sassan jiki na roba ga nakasassu

A kokarin tallafa wa mutanen da suka samu nakasa a dalilin hare-haren Boko Haram, an fara aikin sanya hannaye da kafafu na roba ga irin wadannan mutane a Najeriya.

Dubban mutane ne suka tsinci kansu cikin nakasa ta rasa wani bangare na jikinsu a dalilin hare-hare na tashin bom ko ma gurneti a rikicin Boko Haram. Amma sun kasance cike da murna da farin ciki na samun damar sake amfani da wadannan muhimman sassa na jikinsu bayan mawuyacin halin da suka shiga. kungiyar Jama’atu Izalatu Bidi’ah da hadin gwiwar cibiyar Tolaram ta kasar Indiya suka share musu hawayensu ta hanyar sanya masu hannaye da kafafu na roba.

Fatime Abubakar ta ce murnar ta guda daya ce a wannan rana, ita ce kammala shirin sanya mata kafarta daya da aka yanke a dalilin ciwon sikari. Ya zuwa wannan lokaci dai an tallafa wa nakasassu sama da dubu daya, abin da ke taimaka raguwar nakasassun da rashin sassan jikinsu ya jefa rayuwarsu cikin mawuyacin hali da ma jefasu cikin hali na barace-barace da ake ta kokarin shawo kansa.